Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamnatin Tarayya

এছাড়াও পড়ুন:

Rundunar ‘Yansan Nijeriya Za Ta Gudanar Atisaye Ga Jami’anta a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da atisayen harbe-harbe ga sabbin ‘yan sanda a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.

 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jihar.

 

Ya ce, atisayen zai fara ne daga ranar 19 ga Afrilu zuwa 11 ga Mayu 2025 a kauyen Tsohon Kafi da ke Birnin Kudu.

 

A cewarsa, makasudin bayar da horon shi ne don inganta shirye-shiryen gudanar da aiki, da dabarun sarrafa makamai, da kuma kwarjinin sabbin jami’an ‘yan sandan da aka dauka, a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta himmatu wajen tabbatar da kwarewa da tsaron lafiyar jama’a.

 

Don haka rundunar ta bukaci mazauna kauyen Tsohon Kafi da kewaye da kada su firgita da jin karar harbe-harbe a yayin atisayen.

 

Abdullahi ya ce, za a sanya ido sosai a kan dukkan ayyukan da kuma gudanar da su a cikin yanayi mai aminci da kulawa.

 

Rundunar ta kuma yaba da ci gaba da goyon baya da hadin kan al’umma wajen tallafawa kokarin wanzar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

 

KARSHE/USMAN MZ

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tawagar CPPCC Ta Ziyarci Nijeriya Da Cote d’Ivoire Da Senegal
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Rahoton Hana Shettima Shiga Villa
  • Rundunar ‘Yansan Nijeriya Za Ta Gudanar Atisaye Ga Jami’anta a Jigawa
  • Fani-Kayode ya zargi Isra’ila da Hannu a tashe-tashen hankula a Najeriya
  • Sojojin Nijeriya Sun Yi Lugudan Wuta Kan Sansanin Ƴan Ta’adda A Borno
  • Gwamnatin Sakkwato Ta Siyawa ‘Yan Gudun Hijira Gidan Miliyan 100
  • Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa
  • Tsohon Minista Ya Zargi Isra’ila Da Kasashen Yammacin Turai Da Kitsa Kashe-kashen Rayuka A Nijeriya 
  • Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Taron Ƙarawa Ma’aikatan Jinƙai Sani A Jihar Kano
  • Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ’yan jarida su daina kawo rahoton ayyukan ’yan ta’adda