Kasashen Iran Da Katar Sun Jaddada Muhimmancin Shigar Da Dukkanin Bangarorin Al’ummar Kasar A Cikin Sha’anin Kasar
Published: 27th, March 2025 GMT
Manzon musamman na ministan harkokin wajen Iran a kan Syria, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya gana da karamin minista a gwamnatin kasar Katar inda su ka tattauna halin da ake ciki a kasar Syria, haka nan kuma sun jaddada wajabcin shigar da dukkanin bangarorin al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da gwamnati.
A jiya Laraba ne dai Muhammad Ridha Shaibani ya kai ziyara birnin Doha inda ya gana da ministan na kasar ta Katar Muhammad al-Khalifi domin yin shawara akan Syria.
Shaibani ya bayyana mahangar Iran akan Syria, da ya kunshi ganin an shigar da kowane bangare na al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da kasar, ya kuma zama sun taka rawa wajen ayyana makomar kasar.
A nashi gefen ministan na kasar ta Katar Muhammad al-Khalifi ya yi ishara da rawar da Iran take takawa a cikin wannan yankin da kuma tasirisnta, haka nan kuma ya bayyana wajabcin ci gaba ta tuntubar juna domin musayar ra’ayi akan halin da kasar ta Syria take ciki.
Haka nan kuma bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashensu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Da Malaysia Za Su Samar Sabbin Shekaru 50 Masu Muhimmanci Na Dangantakar Kasashen Biyu
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki kasar Malaysia daga ranar 15 zuwa 17 ga wata. Inda bangarorin biyu suka amince da gina al’ummar Sin da Malaysia mai kyakkyawar makomar bai daya bisa manyan tsare-tsare da samar da wasu sabbin shekaru 50 masu muhimmanci na dangantakar da ke tsakanin Sin da Malaysia.
A ra’ayin Xu Liping, masani mai nazarin harkokin kudu maso gabashin Asiya na cibiyar kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin, daukaka matsayin dangantakar da ke tsakanin Sin da Malaysia, na nufin cewa, an kara samun amincewar juna bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, kana ana ci gaba da fadada moriyar juna. Hakan zai taimaka wa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban zuwa wani sabon matsayi, da kafa ma’auni wajen yin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen ASEAN, da sa kaimi ga hadin kai da hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, da kiyaye kwanciyar hankali da wadata a duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp