Sojojin Iran: Gwagwarmaya Ce Kadai Hanyar Warware Matsalar Falasdinu
Published: 27th, March 2025 GMT
Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya.
Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci, da amfani da karfi a kansu, da kuma yin barna a masallacin Kudus, da majami’u, makarantu, asibitoci da kuma cibiyoyin MDD, da kuma shiru din da duniya ta yi, hakan yana nufin cewa ‘yan sahayoniya masu aiki da duk wata ka’ida ko doka ta kasa da kasa balle kuma halayyar kwarai, a dalilin hakan, hanya daya tilo da za a iya sauya wannan yanayin shi ne ci gaba da gwgawarmaya, sannan kuma da samun goyon bayan al’ummar duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa; A wannan lokacin na jajiberin ranar Kudus,al’ummar Falasdinu suna cikin mawuyacin yanayi na cin zali da nuna karfi akansu da ‘yan sahayoniya suke yi ta hanya mafi muni, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar dubban Falasdinawa da kuma jikkatar wasu dubu dubatar, daga cikinsu da akwai kananan yara, mata da kuma fararen hula.”
Bayanin sojojin na Iran ya yi kira ga dukkanin ‘yantattun mutane a duniya da su fito domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu da ake cin zalinsu, tare da kara da cewa, al’ummar Iran ma’abota juyin juya hali za su fito a ranar Kudus ta duniya domin nuna kin jinin zalinci irin na ‘yan sahayoniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jerin Gwanon Ranar Kudus Na Ci Gaba Da Gudana A Kasashen Duniya
Ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya.
Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya.
Marigayi Imam Khomeni ne ya ayyana ranar karshe ta kowane Radan a matsayin ranar Kudus ta duniya tun fiye da shekaru 40 da suka gabata, kuma ana ci gaba da gudanar tarukan wannan rana a kowace shekara a Iran da sauran sassa na duniya.