Sojojin Sudan Suna Ci Gaba Da Samun Nasara A Akan Dakarun Kai Daukin Gaggawa
Published: 27th, March 2025 GMT
A yau Alhamis sojojin na kasar Sudan sun sanar da abinda su ka kira; Yin shara a cikin birnin Khartum, domin gano inda gyauron mayakan dakarun rundunar sa-kai suka buya.
Haka nan kuma sojojin na Sudan sun sanar da sakin farsunoni masu yawa da rundunar kai daukin gaggawa din suka tsare su, a lokacin da suke rike da birnin na Khartum.
Sojojin kasar ta Sudan sun nuna shugaban majalisar sojan kasar Janar Burhan a cikin fadar shugaban kasa, inda ya sanar da cewa; An ‘yanto da Khartum.
A karon farko jirgin Janar Burhan ya sauka a filin saukar jiragen sama na Khatrum, tun bayan da yaki ya barke.
Tun a jiya Laraba ne dai sojojin na Sudan su ka sanar da shimfida ikonta akan filin saukar jiragen sama na Khartum wanda shi ne tunga ta karshe da ta saura a hannun rundunar kai daukin gaggawa.
Kwamandan rundunar sojan Sudan da take fada a birnin na Khartum Lafatnar kasar Abdurrahman al-Bilawi ne ya sanar da cewa, an shimfida iko a cikn filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na birnin Khartum.
Har ila yau kwamandan sojan ya kuma bayyana cewa, a yanzu haka suna cigaba da faraurar mayakin “Rundunar Kai Daukin Gaggawa”da su ka saura a cikin binin Khartum.
Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai sojojin na Sudan su ka kwato fadar shugaban kasa wacce ta dauki shekaru biyu a hannun rundunar kai daukin gaggawa, haka nan kuma babbar cibiyar soja da tsakiyar birnin Khartum da can ne ma’aikatu da dama suke.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: rundunar kai
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Nijeriya Sun Yi Lugudan Wuta Kan Sansanin Ƴan Ta’adda A Borno
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp