Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bukukuwan Sallah na bana, saboda bukatar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
A wata sanarwa da aka fitar, Sarkin ya bayyana takaicinsa kan matakin amma ya jaddada cewa, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne babban abin da ya sa a gaba.
Sarkin ya ce, “Bisa umarnin da jama’a suka ba mu da kuma jajircewar da muka yi na ba su kariya, mun ga ya dace mu janye duk wani shiri da aka yi na bukukuwan Sallah bisa la’akari da halin da ake ciki.”
Ya kara da cewa, tuntubar da aka yi da manyan malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki sun yi tasiri a kan shawarar.
Ya kuma jaddada cewa, duk da cewa bikin Sallah al’ada ce mai kima, bai kamata ta zo da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.
Name(required) Email(required) Website MessageSubmit
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aminu Ado Bayero Jihar Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiyya da Iran sun jaddada aniyar fadada alakar soji a tsakaninsu
Iran ta jaddada shirinta na fadada huldar soji da kasar Saudiyya a wani bangare na batutuwan da ziyarar ministan tsaron kasar Saudiyya Tehran ta kunsa.
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri ya shaidawa Yarima Khalid bin Salman a Tehran a wannan Alhamis cewa “Kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da sojojinsu za ta kawo yanke kauna ga makiyanmu da kuma sanya farin ciki ga abokanmu da sauran musulmi”.
Bagheri ya godewa Saudiyya a kan halartarta a matsayin mai sa ido a babban atisayen sojojin ruwa na tekun Indiya (IONS), wanda aka fi sani da IMEX 2024.
Iran, Rasha, da Oman ne suka gudanar da atisayen a tekun Indiya, tare da halartar tawagogin masu sa ido daga kasashe da dama da suka hada da Saudiyya, Indiya, Thailand, Pakistan, Qatar, da Bangladesh.
Yarima Khalid ya bayyana godiyarsa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma babban hafsan sojin kasar bisa kyakkyawar tarba da suka yi masa tare da tawagarsa a birnin Tehran, yana mai cewa: “karamcin da kuk a yi mana yana nuna kyakkyawar alaka mai karfi da ke tsakaninmu”.