Majalisa ta janye ƙudirin tuɓe wa matakaimakin shugaban ƙasa da gwamnoni rigar alfarma
Published: 27th, March 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta janye ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu.
Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar.
Sallah: Yadda ake shirin caɓa ado duk da tsadar kaya Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan NajeriyaƘudurorin biyu na cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a jiya Laraba.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudurin janyewar.
Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya ce an ɗauki matakin janyewar ne domin bayar da damar yin muhawara kan ƙudurorin bayan cece-kucen da hakan ya haifar a faɗin ƙasar.
Ƙudurorin na daga cikin gwamman ƙudurorin da majalisar ke nazari a kansu, a wani ɓangare na yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999.
Aminiya ta ruwaito cewa, majalisar ta janye ƙudirin ne bayan gwamnatocin jihohin sun bayyana adawarsu kan matakin da ke neman tuɓe musu rigar alfarmar da ke bai wa gwamnoni da mataimakansu da kuma mataimakin shugaban ƙasa kariya daga fuskantar tuhuma kan laifuka.
A ranar Larabar da ta gabata ce ƙudirin ya samu karatu na biyu a zauren majalisar, ƙarkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai
এছাড়াও পড়ুন:
Dole Kwankwaso Ya Nemi Afuwarmu Kafin Ya Komo APC
Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya fitar da wata sanarwa mai ƙarfi game da yiwuwar dawowar wasu shugabannin siyasa cikin jam’iyyar. A lokacin ganawar da manema labarai a Kano, Abbas ya bayyana cewa APC ba za ta karɓi mutane da hukumomin yaƙi da cin hanci kamar EFCC da ICPC ke bincike ba.
Wannan sanarwa ta zo ne a yayin da jita-jita da ake cewa wasu daga cikin mambobin jam’iyyar NNPP, musamman waɗanda ke cikin rukuni na Kwankwasiyya, suna duba yiwuwar komawa APC.
El-rufa’i Ba Zai Halarci Taron Jam’iyyar APC Na Kasa Ba, Kuma Ganduje Na Nan A Shugabanci NNPP Ta Mutu, Kwankwaso Zai Sake Dawowa APC – GandujeAbbas ya bayyana cewa duk wanda ke son dawo wa jam’iyyar dole ne ya nemi afuwa daga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, bisa maganganun cin mutunci da aka yi a baya akan su da jam’iyyar.
Masu fashin baƙin siyasa na ganin cewa wannan magana ta Abbas tana nufin shugaban Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ake zargin yana cikin tattaunawar yiwuwar sauya sheƙa. Wannan furucin na shugaban APC na Kano ya janyo muhawara game da yadda siyasa da daidaiton ra’ayi za su iya faruwa a cikin tsarin siyasar Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp