Sin Za Ta Ci Gaba Da Samar Da Kyakkyawan Yanayin Kasuwanci Da Ya Dace Da Kasuwa Da Doka
Published: 28th, March 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin He Yadong, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da ya dace da kasuwa, da doka da kuma mizanin kasa da kasa.
He Yadong ya bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum, inda ya ce, a wannan lokaci da ake ciki, wasu manyan jami’an kamfanonin kasa da kasa na kawo ziyara kasar Sin.
Bugu da kari, He Yadong ya ce, bangaren Sin ya tsaya tsayin daka kan adawa da matakin karin haraji da bangaren Amurka ya dora wa Sin, yana kuma adawa da siyasantar da batun tattalin arziki da cinikayya ko amfani da shi a matsayin wani makami.
Game da kakaba karin haraji da bangaren Amurka ya yi, kakakin ya ce bangaren Sin ya riga ya shigar da kara a karkashin tsarin warware rikici na hukumar WTO, kuma zai ci gaba da bin matakai bisa ka’idojin WTO.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Farashin fetur ya ƙaru sakamakon hana Dangote mai a Naira
Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa.
A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira.
Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin MusulmiWannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.
Rahotanni sun nuna cewa farashin ya fi ƙaruwa a Arewa, yayin da Legas ke da mafi ƙarancin farashi.
Kamfanin MRS Oil & Gas na jigilar mai daga Legas zuwa sassa daban-daban na ƙasar.
Duk da haka, ba a bayyana takamaiman wajen da aka sayo sabon man fetur ba, amma yanzu ana sayar da shi a farashin da ya bambanta da na baya.