Kasar Sin Na Adawa Da Kara Yawan Kamfanoninta Cikin Jerin Wadanda Amurka Ta Takaita Fitar Da Kayayyakinsu
Published: 28th, March 2025 GMT
Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana matukar adawa da yunkurin Amurka na kara yawan dozin-dozin na kamfanoninta a cikin jerin kamfanonin da aka takaita fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje.
Jami’in, wanda ya bayyana haka a ranar Larabar nan, ya ce, matakin na Amurka ba komai ba ne illa murkushewa da kuma takura wa wasu kamfanonin kasashen ketare, tare da danne hakkokin sauran kasashen duniya na samun ci gaba.
Ya kara da cewa, matakin zai yi kafar ungulu ga kokarin warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa, kuma kasar Sin tana kira ga Amurka da ta gaggauta kawo karshen kurakuran da take tafkawa, kana ya ce, kasar za ta dauki matakan da suka dace don kiyaye hakkoki da muradun kamfanonin Sinawa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Shugaban CMG Ya Gana Da Ministar Raya Al’adu Ta Rasha
Yau Juma’a, shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG Shen Haixiong, ya gana da ministar raya al’adu ta kasar Rasha Olga Lyubimova dake ziyara a kasar Sin.
Shen Haixiong ya ce, yana maraba da Rasha ta shiga a dama da ita cikin bikin fina-finai na kasa da kasa da 0za a yi a kasar Sin a bana.
A nata bangare, Olga Lyubimova ta ce, a shekarun baya bayan nan, Rasha da Sin suna kara musaya a fannoni daban-daban, ciki har da fina-finai, kuma sun samu kyawawan sakamako. Ta kara da cewa, tana fatan bangarorin biyu za su zurfafa hadin gwiwarsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp