NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah
Published: 28th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Lokutan sallah su ne lokuta na farin ciki, godiya ga ni’imar Allah, da kuma ibada.
A wannan lokaci, yana da muhimmanci a tabbatar da ayyukan da ake aikatawa sun kasance masu inganci da dacewa da koyarwar addini.
NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar BiriAmma mene ne ya kamata musulmi su yi kafin da kuma ranar sallah?
Ta wacce hanya za a tabbatar da zaman lafiya da tsari yayin bukukuwan sallah?
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari kan muhimman abubuwan da Musulmi ya kamata su aikata kafin da kuma lokacin sallah.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: abubuwa Najeriya a yau
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya : Mutum 56 suka mutu a harin Benue
Hukumomi a jihar Benue dake Najeriya sun ce adadin wadanda suka mutu a harin da ‘yan bindiga suka kai a hukumomin Ukum da Kogo ya kai 56.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, a wata ziyara a yankin ya shaidawa manema labarai cewa adadin wadanda suka mutu a harin ya kai 56.
”A yanzu, mutum 56 ne suka mutu wadanda ba su ji ba su gani ba, da suka hada da iyaye da maza da mata da kananan yara”, in ji shi.
Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar matakai domin kawo karshen hare-hare a jihar.
Gwamnan ya ce tuni gwamnatin jihar ta kara tura jami’an tsaro zuwa yankunan domin kwantar da hankula.
Harin na zuwa ne kimanin mako biyu bayan wasu yan bindiga sun kashe fiye da mutum 100 a wasu hare-hare a jihar Plateau mai makwabtaka.