’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano
Published: 28th, March 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano,m, ta ƙwato kuɗi Naira 4,850,000 tare da mayar da su ga wani mutum da aka sace, bayan sun ceto shi.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an yi garkuwa da mutumin ne a garin Zakirai, a Ƙaramar Hukumar Gabasawa.
An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isuhu Yellow a Zamfara Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a KebbiMasu garkuwar sun fara neman kuɗin fansa Naira miliyan 15 kafin daga bisani jami’an tsaro suka shiga lamarin.
“Bayan samun labarin garkuwar, jami’anmu sun ƙaddamar da bincike, inda suka kama mutum biyar da ake zargi, sannan suka ceto wanda aka sace a ranar 17 ga watan Maris,” in ji sanarwar.
An mayar da kuɗin ne ta hannun shugaban Ƙaramar Hukumar Gabasawa, Sagir Usman Abubakar, wanda ya bayyana godiyarsa a madadin wanda aka sace da mutanen yankin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai, ta hanyar kai rahoton duk wani abu da suke zargi domin daƙile ayyukan miyagu a Kano.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya
A Bikin Yawan Sallah na Jafi da aka yi a fadar Sarkin Gombe, Mai Martaba Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya yi kira ga manoma da makiyaya da su zauna lafiya da juna.
Sarkin ya ce zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaba, kuma haɗin kai tsakanin manoma da makiyaya zai hana rikice-rikice da ke barazana ga jihar.
Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina“Ina roƙon manoma da makiyaya da su zauna lafiya don guje wa rigingimu.
“Kowa yana da haƙƙin tabbatar da zaman lafiya domin hakan na kawo ci gaban tattalin arziƙi da walwalar al’umma,” in ji Sarkin.
Haka kuma, ya tabbatar da cewa masarautar Gombe za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin jihar domin tabbatar da tsaro mai ɗorewa.
Sarkin ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa ƙoƙarinsa na inganta rayuwar al’umma da ɗaukar matakan tsaro, musamman samar da motocin aiki ga jami’an tsaro.
Bikin hawan sallah na Jafi ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da Gwamnan Jihar Gombe da wasu manyan jami’an gwamnati, inda aka jaddada buƙatar haɗin kai da zaman lafiya a jihar.