Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Mayarwa Shugaban kasar Amurka Donal Trump amsar wasikarsa ga kasar danagne da shirinta na makashain Nulkiya ta hanyar kasar Omman.

Aragchi ya bayyana haka a jiya Alhamis a lokacinda yake hira da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran.

Ya kuma kara da cewa a cikin wasikar dai gwamnatin JMI bayyanawa shugaban kan cewa tana ganin bazata iya shiga tattaunawa gaba da gaba da Jami’an gwamnatin kasar Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, saboda halayen gwamnatocin Amurka a baya dangane da shirin.

Daga ciki Iran ta dauke shekaru biyu cutar tana tattauna batun wannan shirin da manya-manyan kasashen duniya daga ciki har da kasar Amurka,  aka cimma yarjeniya a shekara ta 2015, kuma har an fara aiwatar da yarjeniyar ta JCPOA, amma gwamnatin Amurka ta lokacinda wanda shugaba mai ci yake jagoranta ta fice daga cikin yarjeniyar ba tare da wani dalili ba, sannan ta dorawa Iran sabbin takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasar da nufin tilasta mata da sake wata tattaunawa  da ita. Waya ya sani mai yuwa da sake saba alkawalin da aka cimma da ita a wannan karon ma, bayan wancan?. Amma ta kasa samun nasara har ta sauka.

Banda haka a lokacinda wannan gwamnatin ta zo kan karagar shugabancin Amurka ta fara kara dorawa JMI wasu karin takunkuman tattalin arziki kafin ma ta gayyana kasar zuwa tattaunawa.

Wannan ya nuna cewa ba tattaunawa take bukata ba, sai dai tursasawa. Wanda kasar Iran baza ta taba amincewa da haka ba.

Sannan idan Amurka ta na son shiga tattaunawa da Iran kan shirinta na makamashin Nukliya to a halin yanzu ma tana tattaunawa da kasashen turai uku kan shirin nata. Sai ta shigo.

 

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Amurka

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka ta sanar da cewa za ta rage yawan sojojinta a Syria da rabi

Amurka ta sanar cewa ta rage yawan sojojinta a kasar Syria da rabi, tana mai cewa ta yi nasarar yaki da kungiyar IS, duk da cewa kungiyoyin masu da’awar jihadi na ci gaba da fafutuka a wannan kasa mai rauni.

Wannan shawarar ta zo ne kusan watanni uku bayan hawan Donald Trump kan karagar mulki, bayan da ya dade yana adawa da kasancewar Amurka a can.

Amurka dai ta shafe shekaru da dama tana da sojoji a Syria, a matsayin wani bangare na kawancen kasashen duniya da ke yaki da ISIS.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon Sean Parnell ya fitar, ya ce za a rage yawan dakarun Amurka a Siriya zuwa kasa da dakaru 1,000 a cikin watanni masu zuwa daga kusan 2,000.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Gayyaci Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Aragchi Taron Makamashin Nukliya A Amurka
  • Idan Shugaban Kasar Siriya Mai Ci Ya Taka Kasar Iraki Ana Iya Kama Shi
  •  Abbas Arakci: Tattaunawa Da Amurka Ta Hanyar Shiga Tsakanin Oman Ta Shiga Sabon Zango
  • News Fox: Sau 6  Yemen Ta Kakkabo Jiragen Amurka Samfurin Mq 9 A Karkashin Gwamnatin Trump
  • An Fara Bikin Ranar Sojin A Iran 18 Ga Watan Afrilu Tare Da Gudanar da Fareti A Gaban Shugaban Kasar
  • Iran Da Amurka Za Su Ci Gaba Da Tattaunawa Kan Shirin Nukiliyar Tehran
  • Iran da Amurka na shirin tattaunawa ta biyu a birnin Rome
  • Amurka ta sanar da cewa za ta rage yawan sojojinta a Syria da rabi
  • Iran Tace Yarjeniya Da Amurka Mai Yuwa Ne Idan Da Gaske Take
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Iran Da Saudiyya Za Su Iya Magance Yawancin Matsalolin Yankin Gabas Ta Tsakiya