Iran Ta Gudanar Da Faretin Jiragen Ruwa A Tekun Farisa Da Kuma Tekun Caspian Don Raya Ranar Kudud Ta Duniya
Published: 28th, March 2025 GMT
Jiragen ruwan yaki na dakarun juyin juya halin musulunci IRGC a nan Iran, kanana da manya-manya, har’ila yau da na masu sa kai sun gudanar da faretin jiragen ruwan yaki don raya ranar Kudus ta duniya kwana guda kafin ranar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dubban jiragen yaki da na masu sa kai a tekun Farisa da ke kudancin kasar da kuma tekun Caspian da ke arewacin kasar suna jerin gwano a cikin ruwayen yankunansu don raya wannan ranar.
Dakarun IRGC sun gudanar da wannan atisai ne a jiya Alhamis, don nuna goyon bayansu ga Falasdinwa musamman a Gaza, wadanda a halin yanzu, sojojin HKI sun yi masau kawayya, sun hana shigowar abinda da abinsha cikin yankin sama da wata gusa, sannan suna binsu suna kashewa.
Majiyar dakarun IRGC ta bayyana cewa sama da jiragen ruwa da kwale-kwale kimani 3,000 ne suka fito don tallafawa falasdinawa musamman a Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan, wadanda sojojin yahudawa suka kashewa a ko wace rana.
Labarin ya kara da cewa, a kudancin kasar an baje kolin katafaren jirgin ruwa mai daukar jirage yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, mai sun a ‘shahida beheshti’, jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa suna sauka su kuma tashi a kan wannan jirgin yakin.
HKI dai wacce take samun tallafin kasashen yamma musamman Amurka suna mamaye da kasar Falasdinu fiye da shekaru 70 a halin yanzu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?
Masu wannan fahimta sun yi imanin cewa duk lokacin da mutum ya ji baya son wani abu to a wurinshi wannan abin ba mai kyau ba ne. Haka nan kuma duk lokacin da mutum ya ji cewa ga wani abu amma shi ne ya kwanta mashi, toh wannan abin shi ne mai kyau.
Babban misalin da wadannan masu ra’ayi suke jaddadawa da nanatawa a kullum shi ne cewa a lokacin da mutum ya yi tsammanin cewa wani abu na da kyau a ra’ayinshi, to idan ya je cikin wata al’ummar zai tarar da cewa wannan abin barna ko wani abin ki. Misali da shan giya, caca da sauransu.
Da irin wannan nazari ne aka samar da mafi shaharan nazariyyar nan ta NIHILISM, wanda ya zo da wasu ‘yan sauye-suye. Fahimtar ta Nihilism ta ce, sam babu wata doka da za ta iya bambancewa tsakanin abu mai kyau da mara kyau. Don haka ta hanyar ra’ayi da mahangar mutum ne kawai zai iya bambancewa tsakanin mai kyau da marar kyau.
Masu fahimta irin ta Nihilism sun tafi a kan cewa, dabi’ar mutum da yanayin mu’amalarsa da mutane ne kadai za ta iya ayyana nagartacciyar rayuwa ya ke yi ko akasinta. sannan kuma zantukan yabo ko zagi daga makusantan mutum su ma za su iya fayyace irin rayuwar da ya ke yi, ma’ana, abubuwan da suke fadi a kan shi.
Kowanne mutum yana dauke da wasu nauyayen abubuwa na irin dabi’un da ya kamata ya nunawa makusantanshi. Misali da akwai hakkoki na dabi’a da su ka wajaba akan shi wadanda da su ne zai mu’amalanci iyayensa. Haka nan shugaba akwai dabi’o’in da su ya kamata ya mu’amalanci mutanen da ya ke shugabanta.
Bayan samuwar wannan fanni na Nihilism, wanda shi ma ya zo da gudummawarsa dangane da yadda mutum zai gabatar da nagartacciyar rayuwa, sai masanin falsafa Plato ya bulla da sabon nazari wanda kaitsaye ya ke kalubalantar tushen nazariyyar Nihilism din. nazarin na shi ne ya yi kaurin suna har a ke yi masa lakabi da PLATONISM.
Plato cewa ya yi bayani kan wata babbar hanya da mutum zai bi ya gudanar da nagartacciyar rayuwa, inda a takaice ya ce, ‘Mutum ya nemi ilmi’. Ya ci gaba da cewa, a dai dai lokacin da mutum ya samu ilmi ya fahimci me ake nufi da nagartacciyar rayuwa, lallai babu wani abu da zai hana shi bin wannan hanya.
Plato ya ce aikata alfasha da masha’a duk suna aukuwa ne saboda karancin ilmin mai aikata su. Idan mutum ya fahimci ga gaskiya, ita zai bi domin gudanar da nagartacciyar rayuwa.
An zargi wannan nazarin da cewa, ta ya ya mutanen da ke da mabanbantan fahimta za su iya yin ilmin da za su yi nagartacciyar rayuwa? Sai ya ci gaba da bayanin cewa mutum duk ilminsa ba zai iya gano yadda ya kamata ya yi rayuwa ta gari ba, har sai ya samu horo na musamman dangane da abin da ake nufi da abu mai kyau da mara kyau.
Mutumin kuma da bai da kwakwalwar da za ta iya fahimtar karatu sai ya rika koyi da wadanda su ke da ilmi da horon gudanar da rayuwa mai kyau.
Plato ya ce, lura da tarbiyyar yara tana da muhimmanci wurin basu horo da ilmi, wanda kuma hakan zai sa su samu halayen kwarai da dattako. Yana da kyau al’umma ta yi kokarin ganin cewa wadanda ke mulkarsu (shugabanni) mutane ne masana, masu halin dattako da natsuwa da zurfin ilmi.
Lokacin da nazariyyar Platonism ta bayyana ta zama tamkar kishiya ga Nihilism. Domin kai tsaye nazarin ya yi dirar mikiya ne akan Nihilism da ra’ayoyinsa. kuma wannan tunani na Platonism ya samu karbuwa dari bisa dari a falsafar addinai. Sai dai wasu ‘yan bambance-bambance da ba za a rasa ba, da kuma gyare-gyare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp