Jagora Ya Yi Kira Ga Iraniyawa Su Fito Don Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zargar Ranar Kudus Ta Duniya
Published: 28th, March 2025 GMT
Imam sayyid Aliyul Khamina’ie Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yayi kira ga mutanen kasar su fito kwansu da kwarkwatansu don halattar zanga-zangar ranar Kududs ta duniya a yau Jumma’a.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Alhahamis da yamma.
Ranar Qudus ta duniya dai, rana ce wacce Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya ware a ko wace ranar Jumma’a ta karshe na watan Ramadan mai alfarma, na ko wace shekara, don nuna goyon bayan ga al-ummar Falasdinu wadanda ake zalunta, saboda mamayar kasarsu da aka yi. Sannan da kasancewar masallacin Al-Aksa a birnin Qudus al-kiblar musul ce da farko, wanda yake hannun yahudawan sahyoniyya a halin yanzu.
A bana wannan zanga-zangar za’a yi ta ne a dai-dai lokacinda yahudawan suke kissan kiyashi wa falasdinawa a Gaza a karkashin yakin tufanul aksa, wanda ya zuwa yanzu sun kashe falasdiyawa fiye da dubu 50 a yaynsa wasu fiye da dubub 120000 suka ji raunin..
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya : An samu hargitsi a yayin jerin gwanon ranar Kudus a Abuja
Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 20 ne suka mutu sakamakon hatsaniyar da aka samu tsakanin sojoji da masu jerin gwanon ranar Kudus ta duniya a Abuja fadar mukin Najeriya.
Hotunan faifan bidiyo sun nuna yadda masu zanga-zangar ke neman mafaka yayin da karar harbe-harbe ke kara kamari a kusa da su.
An ce an kai gawarwakin mutanen goma sha hudu zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Ana gudanar da tattakin ranar Qudus ta duniya duk shekara a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.