A yayin da watan Ramadan ɗin wannan shekara yake bankwana, ga abubuwan da malamai suka bayyana game da fitar da Zakkar kono, wato Zakatul Fidr ga duk wanda ke da hali.
Sahabi Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) wajbata fitar Zakkar kono domin kankare kurakurai da yasassun maganganun da mai azumi ya yi, sannan sadaka ce ga miskinai.
Daga cikin hikimar bayar da ita, akwai sanya wa miskinai farin ciki ta hanyar samar musu da abin da za su ci a lokacin Ƙaramar Sallah.
Yadda ake fitarwaMutum zai fitar wa kansa da kuma waɗanda yake ciyarwa kamar mata, ’ya’ya da ma’aikata da sauransu idan Musulmai ne.
“Manzon Allah Ya wajabta fitar da zakkar kono ga babba da yaro, ’yantacce da bawa, daga cikin wadanda kuke ciyarwa,” kamar yadda Abdullahi bn Umar ya ruwaito a Hadisi.
Mai fitar da zakkar zai fara ne da fitar wa kansa, sannan sauran mutanen gwargwadon wajibcin ciyar da su a kansa.
Adadin da ake fitarwaKowanne mutum ɗaya za a fitar masa da Sa’i ɗaya, wato Mudun Nabi hudu.
Idan babu Sa’i ko Mudun Nabin awo, ana iya aunawa da tafin hannu.
Malamai sun ce Mudun Nabi ɗaya daidai yake da cikin tafin hannu biyu na matsakaicin mutum.
Abin da ake fitarwaAna fitar da zakkar kono ce daga nau’in ɗanyen abincin mutanen garin.
Ana fitarwa ne daga abin da ya ƙaru a kan abincin rana da yinin mai fitarwa da iyalansa a lokacin.
Lokacin fitarwaMalamai sun bayyana cewa ya halatta a fitar da zakkar tun daga ranar 28 ga Ramadan.
Hadisi ya nuna, “Abauullahi bn Abbas kan ba da ita da kwana ɗaya ko kwana biyu kafin ranar Sallah.”
Amma tana wajaba ne daga safiyar ranar Ƙaramar Sallah, a kuma gama kafin Sallar Idi.
“Wanda ya bayar kafin sallah to zakka ce karɓaɓɓiya, wanda ya bayar bayan sallah kuma to sadaka ya bayar kamar sauran sadakoki.”
Malamai sun ce haramun ne a jinkirta fitar da da ita ba tare da uzuri ba.
Waɗanda ake bai waHadisi ya nuna miskinai ake bai wa.
Wasu malamai na ganin ana iya ba da ita ga sauran mutanen da ake ba wa zakkar farilla (bayi, matafiya, masu bashi a kansu, masu aikin karbar zakka, masu aikin fisabilillahi, wadanda ake kwadayin su musuluntar).
Wanda aka ba wa zakkar shi ma zai fitar, idan har an samu ragowa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ciyarwa Zakkar Kono fitar da zakkar kono a fitar da zakkar
এছাড়াও পড়ুন:
Abin da ya sa nake jin daɗin yadda Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa — Buhari
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana jin daɗin yadda shugaban ƙasar Bola Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa.
Buhari ya ce har yanzu Tinubu bai sauya ba daga tsari da manufofin da jam’iyyar APC ta kafa wanda har ya sanya shi kansa ’yan Nijeriya suka zaɓe shi a 2015.
An ga watan Sallah a Saudiyya Dalilin da Aminu Bayero ba zai iya jagorantar hawan Sallah ba — KurawaBuhari ya bayyana hakan a saƙonsa na taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, wanda ya cika shekaru 73 a doron ƙasa.
Sanarwar da mai magana da yawun Buhari, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, ta ce tsohon shugaban yana alfahari da alaƙarsa da shugaban ƙasar na yanzu.
Sanarwar ta ce Buhari da Tinubu sun gana ta wayar tarho a ranar Juma’a, inda a ciki Buhari ya yi Tinubu addu’ar tsawon rai da ingantacciyar lafiya da, sannan ya yi masa fatan samun nasarar a mulkinsa.
“Idan muka yi wa shugabanninmu addu’a, muna yi wa kanmu ne. Ƙasarmu na buƙatar addu’o’inmu,” in ji Buhari a ganawarsa da Tinubu.
Buhari ya ce shi da iyalansa suna godiya ga Tinubu da sauran jagororin jam’iyyar bisa ƙoƙarin da suka yi wajen kafa jam’iyyar APC, inda har ya samu nasarar zama shugaban ƙasa har sau biyu, bayan ya sha gwadawa a baya ba tare da samun nasara ba.
“Lokacin da ’yan Nijeriya suka zaɓi APC a 2023, zaɓi suka yi domin kafa tubalin sabuwar Nijeriya inda talakawa za su samu damarmakin da suke buƙata, kuma ina jin daɗi har yanzu ba a kauce daga tsarin ba.”