Jihad Islami: Ranar Quds Dama Ce Ta Hadin Kai Tsakanin Al’umma
Published: 28th, March 2025 GMT
Wakilin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad a Tehran ya bayyana cewa: Ranar Qudus wata dama ce ta samar da hadin kai. A wannan rana al’ummar musulmi suna sabunta alkawarin da suka yi da Allah dangane da batun Palastinu.
Ranar Kudus tana hada kai tare da karfafa gwagwarmayar Musulunci a yankin.
Ya ci gaba da cewa, dukkanin bangarori na sun yi imanin cewa, hanya daya tilo ta kubutar da Kudus da kuma ‘yantar da kasar Falasdinu ita ce goyon bayan Kudus da kuma tinkarar mamaye yankunan Falastinu da hakan ya hada da wannan masallaci mai alfarma da yahudawan sahyuniya suke yi.
Ranar Kudus ta duniya ita ce ranar da ke bayyana dukkan sharrin Amurka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma a wannan rana ne ake daga tutar ‘yanci da barranta daga zalunci, inji shi.
Ya kara da cewa, Wasu daga cikin shugabannin kasashen musulmi suna nuna halin ko-in-kula ga Palastinu da kuma halin da al’ummar Palastinu suke ciki, wanda kuma shirunsu nuna goyon baya ne ga zaluncin yahudawa a kan Falastinawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Faransa : An kama wata ‘yar Iran mai goyon bayan Falasdinu
A faransa ana ci gaba da tsare wata ‘yar Iran mai goyan bayan Falasdinu, bis azarginta da iza ta’addanci.
Mahdieh Esfandiari (mai shekaru 35) ana tsare da ita tun ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan kama ta a binrin Lyon, inda ta ke da zama.
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ya yi Allah wadai da kama Mahdieh Esfandiari, yana mai yin Allah wadai da “manufofin kasashen Turai” wanda “ya kunshi murde adawa da “kisan kare dangi” da Isra’ila ta yi a Gaza.
Ya kara da cewa ba a sanar da ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris da kuma iyalan yarinyar ba.
A nasa bangaren, lauyan Mahdieh Esfandiari, Nabil Boudi, ya nuna rashin jin dadinsa kan kamun da aka yi wa wadda yake karewa.