Aminiya:
2025-03-31@06:43:25 GMT

Tinubu zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio

Published: 28th, March 2025 GMT

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu nasarar lashe zaɓe don yin wa’adi na biyu a 2027, duk da ƙoƙarin ’yan adawa na ƙalubalantarsa.

Yayin da yake jawabi a wajen liyafar buɗa-baki da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC (PGF) ta shirya a Abuja, Akpabio ya nuna ƙwarin gwiwa cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da mulki.

Sallah: Hadimin gwamnan Sakkwato ya bai wa magoya bayan APC kyautar N22m ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano

“Za mu dawo a 2027, da sunan Yesu, Amin,” in ji shi.

“Za mu yi wa jam’iyyarmu da Shugaban Ƙasa addu’a. Wa’adin mulkinsa na biyu ya tabbata.”

Liyafar, wacce gwamnonin APC, ’yan majalisa, da ministoci suka halarta, ta zama gangamin siyasa, inda shugabannin jam’iyyar suka jaddada nasarorin Tinubu.

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce APC za ta ci gaba da mulki: “Yunƙurin ’yan adawa na ƙwace mulki daga hannun Tinubu ba zai yi nasara ba.

“Dole mu yi amfani da ‘wa’azin siyasa’ don nuna ci gaban da muka samu.”

Duk da cewa Tinubu bai sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a karo na biyu ba, shugabannin APC sun fara gangamin mara masa baya ta hanyar taruka da nuna goyon baya, yayin da ’yan adawa ke sukar hakan a matsayin kamfe.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Nasara wa adi Zaɓe Zaɓe 2027

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya : An samu hargitsi a yayin jerin gwanon ranar Kudus a Abuja

Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 20 ne suka mutu sakamakon hatsaniyar da aka samu tsakanin sojoji da masu jerin gwanon ranar Kudus ta duniya a Abuja fadar mukin Najeriya.

Hotunan faifan bidiyo sun nuna yadda masu zanga-zangar ke neman mafaka yayin da karar harbe-harbe ke kara kamari a kusa da su.

An ce an kai gawarwakin mutanen goma sha hudu zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Ana gudanar da tattakin ranar Qudus ta duniya duk shekara a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Hamayyar Siyasar A Kasar Turkiya Suna Ci Gaba Da Yin Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati
  • Abin da ya sa nake jin daɗin yadda Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa — Buhari
  • Najeriya : An samu hargitsi a yayin jerin gwanon ranar Kudus a Abuja
  • Rikici Ya Turnuke Jam’iyyar SDP A Yayin Da Aka Samu Shugabanni Bangare Biyu A Kogi
  • Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar
  • Me Ya Sa Fina-finai Masu dogon Zango A Masana’antar kannywood ke Zama Cin kwan Makauniya?
  • Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand
  • An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara
  • Jihad Islami: Ranar Quds Dama Ce Ta Hadin Kai Tsakanin Al’umma