ECOWAS ta gyara cibiyar magance shan miyagun ƙwayoyi a AKTH
Published: 28th, March 2025 GMT
Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta kammala gyara wata cibiya don kula da masu fama da shan miyagun ƙwayoyi a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) da ke Kano, tare da miƙa ta ga asibitin domin amfanin jama’a.
Jami’in ECOWAS mai kula da shirin hana yawaitar shan miyagun ƙwayoyi, Dokta Daniel Akwasi Amankwaah, ya ce wannan cibiya na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar wajen rage yawaitar shan ƙwayoyi da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga masu buƙata.
A yayin bikin miƙa cibiyar, Dokta Amankwaah, ya jaddada aniyar ECOWAS na yaƙi da matsalar shan miyagun ƙwayoyi, inda ta ce duniya ta ɗauki wannan matsala a matsayin wata babbar barazana ga lafiya da zamantakewa.
Ya bayyana cewa bayanan da Hukumar Bincike kan Amfani da Miyagun Ƙwayoyi a Yammacin Afirka (WENDU), ta fitar daga 2018 zuwa 2023 sun nuna ƙaruwar masu shan miyagun ƙwayoyi a yankin, duk da ƙarancin wuraren kula da su.
Saboda haka, ECOWAS ta ƙaddamar da wani shiri tun a 2019 domin taimaka wa membobints wajen kafa ko gyara cibiyoyin kula da masu shan miyagun ƙwayoyi.
Ya zuwa yanzu, an kammala cibiyoyi takwas a ƙasashe shida, inda Najeriya ta samu guda huɗu, yayin da ake ci gaba da aikin wasu uku.
Dokta Amankwaah, ya ce kammala wannan cibiya a AKTH zai taimaka wajen kula da marasa lafiya ta hanyar dabarun kiwon lafiya, wanda zai rage illar shan miyagun ƙwayoyi tare da inganta rayuwar jama’a.
Kwamandan Hukumar NDLEA a Kano, Ahmed Idris, ya ce wannan cibiya wata babbar nasara ce a yaƙi da shan miyagun kwayoyi.
Ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi domin cimma gagarumin nasara.
Shi ma Shugaban AKTH, Abdurrahman Abba Sheshe, ya yaba da wannan tallafi, inda ya ce cibiyar ba kawai al’ummar Kano za ta taimaka ba, har da maƙwabtan jihohi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ECOWAS Miyagun ƙwayoyi shan miyagun ƙwayoyi
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin Jihar Kano.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya fitar a wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar rundunar da ke Bompai a wannan Juma’ar.
Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno ECOWAS ta gyara cibiyar magance shan miyagun ƙwayoyi a AKTHCP Bakori ya ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan ƙaramar sallah da za a soma ranar Lahadi ko Litinin.
Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a jihar, kafin sallah da lokacin bukukuwan bayan sallar.
“Haka kuma an haramta duka nau’ikan hawan sallah da duk wata kilisa ta dawakai ko tseren mota a lokacin bukukuwan sallah ƙaramar da ke tafe,” in ji sanarwar.
’Yan sandan sun ce sun ɗauki matakin ne sakamakon rahotonnin tsaro da suka samu da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, domin tabbatar da zaman lafiyar al’ummar jihar.
Haka kuma ’yan sandan sun shawaraci mazauna jihar da su gudanar da sallar idinsu cikin kwanciyar hankali da lumana, yadda aka saba, ba tare da tashin hankali ba.
“Don haka muna kira ga al’umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa”, in ji sanawar.
Hakan na zuwa ne dai bayan da jama’a suka zura ido suna jiran ganin Sarki Muhammadu Sanusi II zai yi hawan sallah a jihar, bayan Sarki Aminu Ado Bayero ya sanar da janye hawan saboda dalilai na tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ko a bara ma dai sai ’yan sanda suka haramta hawan Sallah a birnin na Dabo a sakamakon taƙaddamar masarautar jihar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.