A Cikin Mako Daya An Yi Asarar Naira Biliyan 365 A Kasuwar Sayar Da Hannun Jari
Published: 28th, March 2025 GMT
A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43.
Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda 60,782 da masu zuba hannun suka yi.
Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818 sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222.
Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune, kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da Bankin Jaiz Plc, sun sayar da shiyar da ta kai ta Naira biliyan 1.621, tare da karin Naira biliyan 3.244 da kuma wata hada-hadar Naira biliyan 1,528.
Hakan ya nuna cewa, an samu karin da ya kai na kaso 49.42 da kuma karin wani kaso 5.11 wanda ya nuna irin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta baki daya a kasuwar a cikin makon.
Kazalika, kamfanin sarrafa abincin dabbobi na Livestock Feeds Plc, ya samu karin farashin shiya mai yawa, inda ya samu kaso 22.16 sai kuma kamfanin Caverton Offshore Support Grp da ya samu farashin shiyar da ta kai karin kaso 15.38.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Asara Kasuwar Hannu Naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Gwarzon gasar Alƙur’ani ya Kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina
Iyayen Abdulsalam Rabi’u Faskari, wanda aka sace tare da mahaifinsa a Jihar Katsina, sun bayyana cewa sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
Abdulsalam, wanda ya lashe gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa da aka gudanar a Jihar Kebbi, an sace shi tare da mahaifinsa da wasu makonni biyu da suka gabata, bayan Gwamnan Katsina ya karrama shi.
Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi. Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin MusulmiMahaifinsa, Malam Rabiu Zakariya Faskari, ya shaida cewa suna tsare a hannun ’yan bindiga a Katsina har sai da wani babban ɗan bindiga mai suna Yellow daga Zamfara ya zo ya karɓe su da ƙarfi.
“Ya yi wa masu garkuwa duka kafin ya tafi da mu,” in ji shi.
Ya ce an yi ciniki kan fansa amma Yellow ya ƙi yarda.
“Muna ta addu’a har ranar Juma’a da aka zo aka ce mu fito mu tafi. Yaransa suka ɗauke mu suka kai mu wani gari, daga nan muka yi tafiyar awa huɗu kafin muka samu mota.”
Malam Rabiu, ya ce da suka hau babur sai direban ya shaida musu cewa an kashe Yellow.
“Ashe mutuwarsa ce ta sa yaransa suka sake mu muka koma gida.”