Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya
Published: 28th, March 2025 GMT
Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya.
A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya.
Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus.
Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis tare da ba da umarnin ƙaddamar da bincike a kai.
Wata sanarwa da Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Edo, Fred Itua ya fitar, ta tabbatar da cewa ’yan sa- kai ne suka kai harin
Sanarwar ta ambato Gwamna Monday Okpebholoce na shan alwashin hukunta “masu laifin.”
“Binciken farko-farko ya nuna cewa matafiya ne da suka taso daga Fatakwal na Jihar Ribas suka ratso ta garin, sai ’yan banga suka kama su da tunanin cewa ɓatagri ne,” kamar yadda Fred Itua ya bayyana.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana adadin mutanen da aka kashe ba a harin, amma ta ce Gwamna Okpebholo ya ziyarci garin a ranar Juma’a, inda ya yi alƙawarin gano waɗanda suke da hannu domin su fuskanci hukunci.
Yayin ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru, Gwamna Okpebholo ya yaba wa shugabannin ’yan arewacin Nijeriya “bisa yadda suka kwantar da al’amarin cikin hikima” in ji sanarwar.
Mutum 16 aka kashe ’yan asalin Jihar Kano — AmnestyƘungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce mutane 16 aka kashe kuma ’yan asalin Jihar Kano ne.
“’Yan sa-kai sun tare matafiyan, suka fito da su daga motarsu, suka yi musu duka, sannan suka cinna musu wuta,” a cewar wani saƙo da Amnesty ta wallafa a shafukan sada zumunta.
Ta ƙara da cewa matafiyan na kan hanyar komawa garinsu na asali ne “domin yin bukukuwan sallah tare da iyalansu.”
Amnesty ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar anhukunta masu hannu a cikinsa.
Kwankwaso ya fusataJagoran jam’iyyar adawa ta NNPP kuma tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi tir da kisan, inda ya nemi a gudanar da bincike.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya bayyana harin a matsayin “rashin adalci”
Ya jaddada cewa duk wani ɗan Nijeriya na da ‘yancin yin tafiya a ƙasar nan ba tare da fargabar cin zarafi ko tsangwama ba.
“Abin da kowa ya sani shi ne, ya zama wajibi a bar ‘yan kasa su yi tafiya a duk faɗin kasar nan ba tare da fuskantar wata barazana ko cin zarafi ba.
“Ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike a kan wannan lamari mai tayar da hankali tare da tabbatar da an hukunta masu hannu a ciki,” in ji Kwankwaso.
Atiku ya bayyana kaɗuwarsaTsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya bayyana kaɗuwarsa tare kiran mahukunta da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace kan lamarin
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce “ina matuƙar baƙin ciki da rahotannin kisan gillar da aka yi wa wasu mafarauta a Jihar Edo.
“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalai da ’yan uwan waɗanda abin ya shafa.
“Wannan mummunan lamari yana buƙatar cikakken bincike domin ganowa da kuma tabbatar da cewa an gurfanar da waɗanda ke da hannu a ciki.”
Atiku ya kara da cewa “kare rayukan waɗanda da ba su ji ba ba su gani ba dole ne ya kasance abu mai muhimmanci.
“Kuma ina kira ga hukumomi da su gaggauta ɗaukar mataki don hana sake afkuwar wannan lamari na ɗaukar doka a hannu.”
A tabbatar an kamo masu hannu a aika-aikar — TinubuShi ma Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan yana mai umartar hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka yi wannan mummunar aika-aikar.
“Ba za a bari miyagu su ci gaba da zubar da jinin ‘yan Nijeriya ba tare da hukunta su ba.
“Dole ne a yi adalci,” a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan sa Kai Arewa Jihar Edo mafarauta Rabi u Musa Kwankwaso
এছাড়াও পড়ুন:
Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu
Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki.
Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia.
Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda lamarin ya shafa.
Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu.
“Kamar yadda aka bayyana a ranar Laraba 26 ga watan Maris 2025, jimillar kuɗin da aka tattara sun kai Naira miliyan 839. Bisa ga kididdiga da aka yi, kowanne daga cikin mutanen da lamarin ya shafa kai tsaye zai karɓi kimanin Naira miliyan huɗu.
“Ga waɗanda suka rasu, za a ba da kuɗin ga iyayensu ko magadansu, yayin da waɗanda suka tsira za su karɓi nasu da kansu.
“Kayan tallafin da aka riga aka tara, musamman abinci da sauran kayayyakin bukata, tuni an raba su ga waɗanda suka shafi lamarin“, in ji shi.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa akalla mutane 210 ne lamarin ya ritsa da su, inda 100 daga cikinsu suka mutu nan take.
“An tabbatar da cewa mutane 33 daga cikin waɗanda suka rasu magidanta ne, kuma 31 daga cikinsu sun bar ‘yaya. Jimillar matan da suka rasa mazajensu sakamakon lamarin sun kai 42, yayin da yaran da suka zama marayu suka kai 133″, in ji Gwamna Namadi.
A yayin jajantawa ga waɗanda lamarin ya shafa, Gwamnan ya yi kira ga direbobin manyan motocin dakon mai da sauran masu amfani da tituna su kasance masu taka tsantsan domin gujewa sake afkuwar irin wannan mummunan lamari.
“Iftila’in da ya afku a Majia ya koyar da mu darussa masu yawa, wanda muke fatan jama’a da masu ruwa da tsaki, musamman ma waɗanda ke harkar sufuri, za su dauki darasi“. Inji shi.
Gwamnan ya kuma shawarci waɗanda suka karɓi tallafin su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata, musamman wajen kafa sana’o’i.
Usman Muhammad Zaria