Taron Boao Ya Sake Ba Duniya Damar Ganin Abubuwa Masu Jan Hankali Game Da Sin
Published: 28th, March 2025 GMT
A yau Juma’a aka kammala taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na kasashen Asiya na Boao. Cikin kwanaki 4, kimanin wakilai 2,000 daga kasashe da yankuna sama da 60 ne suka hallara a lardin Hainan na kasar Sin tare da musayar ra’ayi mai zurfi karkashin jigon na “Gina makomar asiya a duniya mai sauyawa.
A matsayinta na mai masaukin bakin, kasar Sin ta gabatar da shawarwari 4 da suka yi daidai da ra’ayin mahalarta taron. Shawarwarin sun hada da karfafa hadin kai da hadin gwiwa wajen inganta aminci, da inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya ta hanyar bude kofa da dunkulewa, da samar da ci gaba da wadata na moriyar juna, da kiyaye zaman lafiya da tsaro da zaman jituwa.
Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2024, an kafa kusan sabbin kamfanoni 60,000 masu jarin waje a kasar Sin, adadin da ya karu kan na 2023 da kaso 9.9. Haka kuma, cikin shekaru 5 da suka gabata, ribar jarin kai tsaye da aka zuba a kasar Sin ta kai kimanin kaso 9, inda adadin ya shiga cikin wadanda ke kan gaba a duniya. A yayin da ake fama da rashin tabbas a duniya, kasar Sin na kara fadada bude kofarta da ingiza kwanciyar hankali a duniya mai hargitsi. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar RED CROSS Ta Duniya Ta Yi Allawadai Da HKI Saboda Kissan Likitoci 8 A Asbitin Rafah
Kungiyar bada agaji ta RED CROSS ta yi allawadai da HKI saboda kissan likitoci 8 a garin Rafah na kudancin gaza a ranar 23 ga watan Maris da muke ciki.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana fadar haka a jiya lahadi bayanda aka basu daman dauko gawakin likitocin wadanda suka rasa rayukansu a cikin watan Motar amblance ta daular marasa lafiya.
Labarin ya bayyana cewa lokitocin suna kan hanyarsu ta zuwa unguwar Hashasha inda HKI ta kai hare-hare kan Falasdinawa don basu taimakon gaggawa.
Banda haka sai da aka dauki mako guda cur da kashe likitocin kafin sojojin yahudawan su bada damar a dauki gawakin nasu.
Ya zuwa yanzu dai tun bayan fara yakin Tufanul Aksa falasdinawa dubu 50 da kari ne sojojin HKI suka kashe a gaza.