Iran: Ta’addancin sojojin Amurka a kan Yemen ‘barazana’ ne ga zaman lafiyar duniya
Published: 28th, March 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce hare-haren da sojojin Amurka ke kaiwa kasar Yemen da keta hurumin yankunanta barazana ce karara ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Baghaei ya yi tir da hare-haren da Amurka ke kai wa Yemen ba bisa ka’ida ba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da raunata jama’ar kasar tare da lalata kayayyakin more rayuwa na kasar.
Ya ce ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen rashin daukar mataki da kuma yin shiru dangane da farmakin da sojojin Amurka ke kaiwa Yemen.
Ya ce Amurka na ci gaba da kai hare-haren soji kan kasar Yemen tare da kai hari kan kayayyakin more rayuwa na kasar domin daukar fansa kan hadin kan al’ummar Yemen da goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta.
Kakakin na Iran ya ce hare-haren na Amurka cin zarafi ne ga ka’idojin Yarjejeniya Ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma ka’idojin dokokin kasa da kasa.
Baghaei ya dorawa gwamnatin Amurka alhakin aikata laifuka.
Kafofin yada labaran kasar Yemen sun ruwaito a safiyar yau Juma’a cewa, an kai wasu sabbin hare-hare a babban birnin kasar Yemen, inda aka kai hari kan wani sansanin soji a kudancin Sana’a da wasu hare-hare guda hudu.
An kuma kai hare-hare a yankunan da ke kusa da filin jirgin sama na Sana’a, baya ga gundumomi biyu a kudanci da tsakiyar lardin Sana’a.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Yemen
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Gagarumar Zanga- Zanga Ta Ranar Qudus Ta Duniya A Birnin Roma Na Kasar Italiya
A birnin Roma masu goyon bayan al-ummar Falasdinu sun gudanar da zanga-zanga ta goyon bayan Falasdinawa, sun kuma ya allawadai da kungiyar tarayyar Turai da kuma Amurka kan yadda suka kasance manay-manyan masu taimakawa HKI a kissan kiyashin da take aikatawa a Gaza.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa daubban wadanda suka fito kan tituna a tsakiyar birnin Roma na kasar Italiya suna rera taken ‘Free Free Palastine, wato yanci yanci Falasdinusun kammala ba tare da wata matsala ba.
Amma a jami’ar Colombia ta kasar Amurka rikicin rikicin jami’ar tare da masu goyon bayan kasar Falasdinu ya kaiga, shugabar jami’ar ta yi murabus daga matsayinta, don bada dama ga wani sabon shugaba, wanda zia aiwatar da shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na kawo karshen abinda ya kira ‘kin yahudawa a Jami’ar’.
Ya zuwa yanzu dai shugaban ya yanked alar Amurka miliyon 400 don takurawa shugabancin Jami’ar ta kawo karshen gangamin dalibai da kuma malaman jami’ar suke yin a goyon bayan Falasdinawa da samun yencin kasar.
Har’ila yau da goyon bayan yahudawan sahyoniyya a kissan kiyashin da take yi a kissan kiyashin da takewa al-ummar Falasdinu musamman a Gaza.