Manyan Amfanin Gona Biyar Da Ya Kyautu Manoma Su Zuba Hannun Jari A 2025
Published: 28th, March 2025 GMT
Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara:
1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya
Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma wanda ake samarwa a cikin kasar, ya ragu da tan miliyan 1.
Kazalika, a gonar da ake noman Kwakwar Manja, za a iya samar da tan 12.5 a kowace hekta daya a duk shekara. Misali, a 2023 a heckta 20 a cikin shekara daya, an girbe Kwakwar da ta kai kimanin tan 250, inda akalla aka samu ribar kimanin Naira 150,000 na kowanne tan daya, wanda kuma ke nuna karin samun kudin shigar da ya kai Naira miliyan 37.5.
Hakan ya kuma kara nuna yadda aka kara bunkasa samun kudin shiga a shekarar da kimanin Naira miliyan 26.25.
2- Gonar Noman Filanten:
Nijeriya ce kan gaba a duniya wajen noman Filanten, duba da cewa; a duk shekara ana noma amfanin da ya kai kimanin tan miliyan 2.8 zuwa tan miliyan 3.1.
Idan kana da Naira miliyan 5, za ka iya mallakar hekta ta noman Filanten, amma ya danganta da inda gonar taka take.
Haka zalika, bisa bai wa gonar kulawar da ta kamata, a tushe daya na Filanten a shekara, za a iya samar kimanin rassa 10,000.
Sannan, duk Nono daya na Filanten, ana sayar da shi daga Naira 2,000 zuwa Naira 4,000, inda a shekara daya, za a iya tara sama da Naira miliyan 40, wato tun daga wata 18 da aka shuka Irin nata.
Kulawar da ake ba shi a shekara bayan an shuka Irinsa, har zuwa girmansa da fara nunarsa, an kiyasata ana kashe sama da Naira miliyan 2, inda manoman za su iya samun ribar sama da miliyan 18 ko fiye da haka a shekara daya.
3- Gonar Noman Dabino:
Nijeriya ce kan a gaba a Afirka wajen noman Dabino, duba da cewa; an kiyasta cewa, a shekara daya ana noma sama da tan 250,000.
Sai dai, abin takaici a 2024, Nijeriya ta shigo da Dabino daga ketare da ya kai na dala miliyan 17.8, inda kasar kuma ta fitar da Dabinon na kimanin dala miliyan 2,070 kacal.
Amfanin da ake yi da shi a duniya a shekara daya, ya kai akalla na tan miliyan 8.5, inda a gabas ta tsakiya da Afirka ta tsakiya, suka kasance kan gaba wajen nomansa da kuma rabar da shi.
Dabino na kaiwa tsawon shekara biyar kafin ya fara yin ‘ya’ya.
4- Irin Kwaka Na Malesiya:
A cewar wasu bayanai da Hukumar Kula da Samar da Abinci da Aikin Gona ta Duniya (FAO) ta fitar, ta dora Nijeriya kan mataki na 18 wajen noman Kwaka a duniya, duba da cewa; kasar na noma Kwakawar da ta kai kimanin tan 225,526 2021.
Wanda ya zuba hannun jari a fannin, zai iya samun ribar sama da Naira miliyan 36 daga hekta goma da aka noma. Samar da heckta 10 a gonar noman Kwaka, zai kasance daidai da zuba hannun jari na kimanin Naira 26,550,000.
Idan har aka shuka ta, a kowace bishiya daya a shekara za ta iya samar da ‘ya’ya 100 , inda za su kai yawan ‘ya’ya 70 da za a girbe a shekara guda.
Kowane Nono daya na Kwakawar, za a iya sayar da shi kan Naira 900, wanda kuma za a iya samar da kudin shiga kimanin Naira 63,000,000 a shekara daya.
Kazalika, bayan ware kudin aikin da manomi ya kashe, zai kuma iya samun ribar da ta kai ta Naira 36,450,000 a shekara daya.
5- Gonar Noman Kashu:
A cewar wani rahoto da jaridar ‘The Nation’ ta wallafa, sama da hecta 600,000 aka ware domin nomansa, wanda zai iya samar da kimanin tan 220,000 a shekara. Farashin Kashu, ya kai daga tan Naira miliyan daya zuwa Naira miliyan 1.5.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da Naira miliyan a shekara daya kimanin Naira iya samar da a iya samar tan miliyan wajen noman a a shekara
এছাড়াও পড়ুন:
Bankin Zenith Ya Samu Ribar Naira Tiriliyan 3.97
Wannan nasarar ta nona irin namijin kokarinda Bankin ya yi na kara habaka samar wa da kansa kudaden shiga duk da matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta.
Bugu da kari, kadarorin Bankin sun karu zuwa jimmlar kaso 47 daga Naira tiriliyan 20 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 30, a shekarar 2024.
Kazalika, abokan huddar Bankin sun karu zuwa kashi 45, wanda kudaden da suka ajiyarsu ya karu zuwa Naira tiriliyan 22 a shekarar 2024, sabanin yadda ya ke kan Naira tiriliyan 15, a shekarar baya.
Duk da samun hauhawan farashin kaya a kasar, Bankin ya samu karin kudaden shigar Bankin, sun karu zuwa kashi 38.9, sabanin kashi 36.1.
Bankin na da yakinin samun ribar shiyar da ta kai ta Naira 4.00, wadda ta kai jimlar ribar shiyar Naira 5.00 da ya samu a shekara.
Shugaba kuma Manajin Darakta na rukunonin Bankin Dakta Adaora Umeoji, da yake yin bayani kan wannan nasarra da Bankin ya samu ya sanar da cewa, nasarar da Bankin ya samu a shekarar, ta nuna irin jajircewar da Bankin ya ke ci gaba da yi, wajen gudanar da ayyukansa, musamman ta hanyar yin amfani da fasahar zamani.
“Zamu kuma ci gaba da mayar da hankali wajen kara habaka fanninin mu na hada-hadar kudade, kara inganta ayyukan mu da farantawa abokan huddar mu da masu ruwa da tsaki rai,”. Inji Bankin Dakta Adaora.
A cewar Shugaban na rukunonin Bankin na Zenith, za mu kuma ci gaba da kara karfafa wanzar da shugabancin mu a fannin hada-hadar kudade na kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp