Ƙungiyar JNI ta raba wa marayu 50 kayan Sallah a Borno
Published: 29th, March 2025 GMT
Ƙungiyar Jama’atul Nasrul Islam (JNI) , ta raba kayayyaki da sauran kyatuttukan Sallah ga marayu 50 gabanin bikin Sallah ƙarama a garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
An gudanar da bikin ba da tallafin ne a harabar makarantar sakandare ta Bulabulin da ke birnin na Maiduguri.
Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa dokar FIFA a wasanta da OsasunaDa yake jawabi a wajen taron, mataimakin daraktan kungiyar JNI reshen Maiduguri, Malam Ibrahim M.
Ya buƙaci waɗanda suka samu tallafin da su yi amfani da kyaututtukan domin biyan buƙatunsu.
A nasa jawabin, mataimakin sakataren ƙungiyar, Abubakar Abdullahi, ya ce sun yi hakan ne da nufin sanya farin ciki da jin dadi ga yara marasa galihu a lokacin bukukuwan Sallah.
Ƙungiyar ta JNI ta himmatu matuƙa wajen taimaka wa mabuƙata, musamman marayu da ba su da abin dogaro da kai in ji Abubakar.
Ya kara bayyana cewa, an zabo waɗanda suka samu tallafin ne bisa sharuɗan da hukumar gudanarwar ƙungiyar ta gindaya.
A cewarsa, ƙungiyar ta shafe sama da shekaru goma tana gudanar da irin waɗannan ayyuka na agaji.
Abdullahi ya kuma yi kira ga iyaye, hukumomin gwamnati, da shugabannin masana’antu da su haɗa hannu wajen ganin an samu sauƙaƙa rayuwar marayu.
Ya yi nuni da cewa, wannan ƙoƙari na haɗin gwiwa zai taimaka matuƙa wajen tallafa wa yara masu rauni da kuma inganta fahimtar al’umma dangane da zamantakewa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jihar Borno kayan Sallah Marayu
এছাড়াও পড়ুন:
Matar gwamna ta ɗauki nauyin ragon suna da hidimar duk matar da ta haifi ’yan uku a Sakkwato
Uwargidan Gwamnan Sakkwato Hajiya Fatima Ahmad Aliyu ta ɗauki nauyin ragon suna da abinci da kayan barka ga duk wata mata da tahaifi ’yan uku a jihar.
Hahiya Fatima ta sanar da haka ne a ranar Laraba nan a lokacin da ta yi takakkiya takanas zuwa garin Ƙaurar Yabo da ke Ƙaramar Hukumar Yabo domin kai ragunan suna da kayan barka da na suna ga wata mai jego mai suna Malama Bela’u, wadda ta haifi ’yan uku a garin.
Daga cikin kayan da ta kai wa mai jego kyauta, har da buhun abinci goma da akwatunan tufafi da tsabar kudi Naira dubu dari biyar.
A bayanin da mataimaka wa gwamna kan harkokin kafofin sada zumunta, Nasir Bazza, ya fitar, ya ce mutanen ƙauyen sun yi farin cikin ganin matar gwamna a garin, wanda shi ne karo na farko da suka ga matar gwamna a yankin nasu.
Ya ce matar gwamna ta yi alkawalin ci gaba da bayar da irin wannan tallafi ga duk wata mata da Allah ya albrkace ta da samun karuwar ’yan uku a lokaci guda a jihar.