Shugaban CMG Ya Gana Da Ministar Raya Al’adu Ta Rasha
Published: 29th, March 2025 GMT
Yau Juma’a, shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG Shen Haixiong, ya gana da ministar raya al’adu ta kasar Rasha Olga Lyubimova dake ziyara a kasar Sin.
Shen Haixiong ya ce, yana maraba da Rasha ta shiga a dama da ita cikin bikin fina-finai na kasa da kasa da 0za a yi a kasar Sin a bana.
A nata bangare, Olga Lyubimova ta ce, a shekarun baya bayan nan, Rasha da Sin suna kara musaya a fannoni daban-daban, ciki har da fina-finai, kuma sun samu kyawawan sakamako. Ta kara da cewa, tana fatan bangarorin biyu za su zurfafa hadin gwiwarsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sharhi: Taruka Da Gangamin Ranar Quds Ta Duniya 2025
A wannan Juma’a ce 28 ga watan Maris na shekarar 2025, aka gudanar da taruka da jerin wano na ranar Qudus ta duniya wadda ta zo daidai da ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma.
An gudanar da wadannan taruka da jerin gwano ne a kasashe daban-daban da suka hada da wasu kasashen musulmi da na larabawa, har da wasu da wasu daga cikin kasashn ymmacin duniya da kuma na Afirka, ta hanyar shirya gagarumin gangamin da ke jaddada aniyarsu ta tabbatar da al’ummar Palastinu ta samu hakkokinta da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramta musu, tare da nuna cikakken goyon baya ga gwagwarmayarsu ta neman samun wadannan hakkoki nasu.
A safiyar Juma’ar ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta tarukan sun yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da kauyukan kasar zuwa wuraren da ake gudanar da Sallar Juma’a.
A birnin Mashhad da ke gabashin Iran, tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da jerin gwano a wani bangare na tarukan ranar Kudus da aka saba gudanarwa shekara-shekara.
A birnin Tehran fadar mulkin kasar ta Iran haka lamarin ya kasance, inda tun da jijjfin safiya dubun dubatar jama’a suka fara fita domin isa wurare da aka kebance domin taruwa, kamar yadda aka saba a kowace ana taruwa ne babban titin Inqilab, wanda titi ne da ya kai tsawon fiye da kilo mita goma a tsakiyar birnin Tehran, inda jama’a suka cika wannan titi makil a lokacin gudanar da jerin gwanon ranar Quds ta dunya.
A jajibirin ranar ta Quds Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Sayyed Ali Khamenei ya bayyana cewa, tattakin ranar Kudus ta duniya na wannan shekara da yardar Allah zai kasance mafi girma a kan na sauran shekaru da suka gabata.
A cikin wani sakon da ya aike ta gidan talabijin a daren Alhamis, jagoran ya bayyana cewa, wannan rana a ko da yaushe wata alama ce ta hadin kai da karfin al’umma, yana mai bayyana yadda tattakin ke nuni da cewa al’umma na tare da gwagwarmaya a kan muhimman manufofinta na siyasa, da kuma tsayawa tsayin daka wajen kare hakkokin al’ummar Falastinu.
A kasar Iran dukkanin bangarori na al’umma suna halartar gangamin ranar Quds ta duniya, da hakan ya hada da mabiya addinai daban-daban, da sauran bangarori na al’umma da jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa da ma’aikata da ‘yan siyasa da kuma malamai, inda suke haduwa a kan kalma guda guda da manufa guda daya, ita ce nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu, da kuma yin tir da Allawadai da zaluncin Isra’ila a kans, da kuma yin kira da babbar murya a kan wajabcin kare hakkokin wannan al’umma da ake zalunta tsawon shekaru aru-aru.
A sauran bangarori na duniya kuwa, an gudanar da irin wannan gangami da jerin gwano a kasashe daban-daban, yankin Jammu da Kashmir na kasar Indiya, an samu halartar dimbin jama’a da ke daga tutocin Falasdinawa da kuma hotunan masallacin al-aqsa, yayin da suke rera taken ‘Yanci ga Falasdinu.
A kasar Bahrain musamman a yankin Bilad al-Qadeem, mahalarta taron sun daga hotunan Sheikh Isa Qassim, Sheikh Ali Salman, da shahidi Sayyed Hassan Nasrallah, a matsayi alama ta gwagwarmaya da zaluncin Isra’ila da kuma nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.
A kasar Yemen, kwamitin al-Aqsa, ya kebance dandalin Sabeen da ke babban birnin kasar Sanaa, tare da wurare sama da 400 a fadin larduna 14, a matsayin wuraren da aka gudanar da gagarumin gangami na ranar Qudus.
Musulmi da kuma masu fafutukar ‘yanci da kare hakkokin bil adama a duniya suna gudanar da ranar Qudus ta duniya kowace shekara a ranar Juma’ar karshe ta Ramadan, inda suke shirya zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu.
A wasu ƙasashe, ƙungiyoyin zamantakewa daban-daban-ciki har da masana da masu fasaha, suna aiki kafada da kafada don wayar da kan jama’a game da buƙatar tabbatarwa da kiyaye haƙƙin Falasɗinawa ta hanyar gudanar da taruka na kara wa juna sani da laccoci, baje kolin zane-zane, da tattara gudummawa da kayan agaji.
Baya ga sassa na kasashen gabas ta tsakiya da Asia, an gudanar da irin wannan taruka da gangami a wasu kasashen yammacin turai da Amurka da kuma Latin Amurka, da kuma wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, da suka hada da Najeriya, Tanzania, Ghana, Senegal, Mali, Kenya, Afrka ta kudu da sauransu.
Ana gudanar da ranar Qudus ta duniya ne a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan bisa kiran da Imam Khumaini ya yi, wanda shi ne ya jagoranci juyin juya halin Musulunci, sannan kuma yunkuri nasa na ayyana ranar Qudus ta duniya, yana a matsayin wani mataki na kare hakkokin al’ummar Palastinu da ‘yancinsu, bayan shafe tsawon shekaru suna cikin wahala da kangi da hijira da mamaye yankunansu, da kuma tuna da duniya irin wannan mawuyacin halin da Isra’ila tare da taimakon kasashen yammacin duniya suka jefa Falastinawa a ciki.