Leadership News Hausa:
2025-03-31@17:28:24 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [21]

Published: 29th, March 2025 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [21]

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [20] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [19]

Fashin Baƙi:

Maganar da Ibn Juzai ya fadi a kan tawakkali tana bayyana ainihin ma’anar dogaro ga Allah cikin dukkan al’amura na rayuwa, wato samun alheri, da kiyaye shi, da kuma kauce wa masifa, ko kuma fita daga cikin masifa idan ta afku.

Tawakkali yana nufin dogaro ga Allah da zuciya ɗaya tare da yin ƙoƙari da dalilan da Allah ya tanadar don cimma buri. Ba wai kawai mutum ya jingina da Allah ba tare da yin aiki ba, ko kuma ya dogara da aikinsa ba tare da tawakkali ba, sai dai a haɗa su duka.

Bangarorin Tawakkali:
Ibnu Juzai ya kasa tawakkali zuwa manyan bangarori guda biyu:
● Tawakkali wajen samun alheri ko kiyaye shi. Mutum ya riƙa dogara da Allah wajen samun ni’ima kamar arziki, da lafiya, da ilimi, da duk wani alheri.Idan mutum ya sami alheri, to yana buƙatar tawakkali don kiyaye shi, saboda shi kansa alheri yana buƙatar kulawa da albarka daga Allah.
● Tawakkali wajen kawar da masifa ko saukinta bayan ta afku. Idan mutum yana fuskantar wata musiba kamar talauci, ko rashin lafiya, ko wata matsala, zai dogara ga Allah don samun sauki. Idan masifa ta riga ta faru, mutum yana tawakkali wajen samun mafita da sauƙin abin da ya same shi a wurin Allah.

A Musulunci, tawakkali ba yana nufin mutum ya zauna ba tare da yin aiki ba. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Da kun yi tawakkali ga Allah da gaske, da ya ciyar da ku kamar yadda yake ciyar da tsuntsaye. Suna fita da sassafe cikinsu da yunwa, kuma suna dawowa da yamma cikinsu a ƙoshe.” Hadisi ne ingantacce Tirmizi da Ɗabarãni ne suka ruwaito.

Wannan hadisi yana nuna cewa tsuntsaye ba sa zama kawai suna jiran Allah ya ciyar da su, sai dai suna aiki ta hanyar sammako neman abincinsu a wurin Allah. Haka ma mutum yana tawakkali ga Allah amma yana yin kokari da aiki tuƙuro da dogaro ga Allah domin kaiwa ga gaci.

Tawakkali yana daga cikin manyan siffofin muminai kamar yadda Allah Ya ce a cikin Alkur’ani: “Kuma ga Allah kaɗai za ku dogara, idan kun kasance ku mummunai ne” Suratul Mã’idati aya ta 23.

Fa’idojin Tawakkali:

Fa’idodin tawakkali sun haɗa da:
• Samun kwanciyar hankali da nutsuwa.
• Rage damuwa da fargaba.
• Samun kariya daga Allah.
• Samun albarka da nasara a rayuwa.

Bambancin Tawakkali da Riƙon Hannu (Tawãkul):
Akwai bambanci tsakanin tawakkali da tawaakul: Domin tawakkali yana nufin dogaro ga Allah tare da yin aiki. Shi kuma tawãkul k yana nufin nuna jingina ga Allah ba tare da bin tsarin da Allah Ya shimfiɗa na riskar abubuwa ba.

A taƙaice, Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama, yana nuni da cewa tawakkali yana rufe dukkan fannoni na rayuwar mutum wajen neman alheri da kiyaye shi, har zuwa kauce wa masifa da fita daga gare ta. Tawakkali yana buƙatar cikakken imani da Allah tare da bin hanyoyin da suka dace da Allah Ya tsara na samun abubuwan rayuwa. Wannan shi ne ainihin fahimtar tawakkali a Musulunci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki Ramadan dogaro ga Allah Tawakkali yana tawakkali yana da Allah ya da Allah Ya tare da yin

এছাড়াও পড়ুন:

Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah

An fara wallafawa ranar 13 ga Mayu, 2022

A halin yanzu al’ummar Musulmi sun yi haramar fara shagulgulan Karamar Sallar bana bayan kammala Azumin Ramadan.

A kan haka ne muka rairayo muku abubuwan da malamai suka kwadaitar da Musulmai su yi a irin wannan rana ta farin ciki da godiya ga Allah bisa ni’imominsa da kammala azumin Ramadan:

Kabbarori:

Daga lokacin da aka ga jinjirin watan Shawwal (Karamar Sallah) ana so mutum ya rika yin kabbarori a bayyane har zuwa lokacin da za a tayar da Sallar Idi.

Daya daga cikin siffoffin yadda ake kabbarorin shi ne: Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar la ilaha illal Lah, Allahu Akbar Allahu Akbar walil Lahil hamd.

Zakkar Kono:

Wajibi ne ga duk wanda ke da hali ya fitar wa kansa da sauran wadanda yake ciyarwa Zakkar Kono a lokacin Karamar Sallah, kafin a yi sallar idi.

Mutum zai fitar wa kansa da kowane wanda yake ciyarwa Sa’i daya (Mudun Nabi 4) na abin da aka fi amfani da shin a abinci a inda yake.

Malamai sun ce za a iya fitarwa tun biyu uku kafin ranar Sallah, amma wajibcinta na farawa ne daga ranar Sallah.

Ana bayarwa ne kafin sallar idi, wanda ya bayar kuma bayan sallar idi, to ta zama sadaka kamar sauran sakakoki.

Wankan idi:

Ana so mutum ya yi wankan ibada kafin zuwa sallar idi a ranar Sallah. Siffar wankan daya ce da sauran wankan ibada.

Sabbin kaya:

Ana so mai zuwa idi ya sanya sabbin tufafi ko mafiya kyawun kayans.

Sahabin Manzon Allah (SAW), Abdullahi Ibn Abbas (RA) ya ce Manzon Allah na da wata alkyabba da yake sawa a ranar idin Karamar Sallah.

Imam Al-Baihaki ya ruwaito cewa Ibn Umar kan sanya mafiya kyawun kayansa a ranar idi.

Turare:

Ana bukatar maza su fito cikin ado su sanya turare domin tafiya sallar idi.

Cin abinci:

Ana so mutum ya ci abinci kafin tafiya sallar idi a Karamar Sallah.

Hadisi ya nuna Manzon Allah (SAW) yakan ci dabino (adadin mara) kafin ya tafi idi a ranar Karamar Sallah. Wanda bai samu dabino bai zai iya cin wani abun.

Zuwa sallar idi:

An fi so mutum ya taka zuwa masallaci, a kan lokaci, yana tafiya, yana yin kabbarori.

Ana zuwa sallar tare kananan yara da mata har da masu jinin al’ada, amma dai za su kebe daga gefen sahu.

Babu kiran Sallah ko nafila:

Ba a yi wa sallar idi kiran sallah sannan ba a yin nafila – zama kawai za a yi ana kabbarori a jira isowar liman.

Abdullahi bin Abbas ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya yi sallar Idi raka’a biyu, bai yi wata sallah (ta nafila) ba kafinta ko bayanta.”

Jabir bin Abdullahi ya ruwaito Hadisi cewa, ba a kiran sallah ko ikama kafin ko bayan sallar idi.

Siffar sallar idi:

Duk da cewa Sallar Idi ba farilla ba ce, ana yin ta ne a jam’i. Raka’a biyu ce kamar kowace sallah mai raka’a biyu kuma a bayyane ake yin ta jim a lokacin Walha.

A raka’ar farko ana yin kabbarori shida bayan Kabbarar Harama. Raka’a ta biyu kuma ana yin kabbara biyar bayan kabbar mikewa zuwa raka’ar.

Sauraron huduba:

Bayan an idar da sallar idi ana bukatar masallata su jira su saurari hudubar liman, kuma laifi ne yin magana a yayin da ake huduba.

Taya murna:

Ana bukatar Musulmai su taya juna murna da fatan alheri a ranar Sallah.

Jubayr ibn Nufair ya ruwaito cewa Sahabbai kan yi wa junansu addu’ar Allah Ya karba musu ibadun da suka yi gabanin ranar.

Sauya hanya:

Koyarwar Manon Allah (SAW) mutum ya sauya hanya idan zai koma gida daga sallar idi.

Zumunci:

Sada zumunci da faranta wa juna rai da abubuwan alheri na daga cikin abubuwan da ake bukata a ranar idi.

Barka da Sallah!

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Azumin Sitta Shawwal a Musulunci
  • Wani Asbiti A Amurka Ya Kori Wata Likita Daga Aiki Bayan Ta Yi Allawadai Da Yahudawan Sahyoniyya
  • Gwarzon gasar Alƙur’ani ya Kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina
  • Eidl Fitr: Gwamna Dauda Lawal Ya Buƙaci A Samu Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi
  • Miji ya kama matarsa da kwarto ta na’urar drone
  • Hezbulla: Iran Ce Babbar Mai Goyon Bayan Al-Ummar Falasdinu
  • Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah
  • JIBWIS Giwa Ya Bukaci Al’ummar Yakawada su Rike Darussan Al-Qur’ani