Aminiya:
2025-03-31@19:22:14 GMT

An kashe mutum 10 a wani sabon hari a Filato

Published: 29th, March 2025 GMT

Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon harin da wasu mahara suka kai wa al’ummar Ruwi da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato.

Maharan sun kai harin ne a daren ranar Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mutanen da suka halarci wata jana’iza da misalin ƙarfe 9:30 na dare.

’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara

Wani mazaunin yankin ya ce: “Mummunan hari ne. Sun zo kwatsam suka fara harbi. Muna roƙon hukumomin tsaro da su ɗauki mataki don kare al’ummarmu.”

Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da faruwar harin, amma ba ta bayyana adadin waɗanda suka rasu ba.

Kakakin rundunar, DSP Alabo Alfred, ya ce, “Kwamishinan ‘yan sanda ya tura ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki don wanzar da zaman lafiya.

“Za mu tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan aika-aika sun fuskanci hukunci.”

Gwamnatin Jihar Filato ta yi Allah-wadai da harin.

Kwamishiniyar Yaɗa Labarai ta jihar, Joyce Ramnap, ta tabbatar wa jama’a cewa ana ɗaukar matakan kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare.

“Gwamnati ba za ta lamunci kashe rayukan ‘yan ƙasa ba. An umarci hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hari

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas ta yi Tir da kakkausar murya da harin Isra’ila kan masu aikin ceto a Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan kungiyoyin kare fararen hula da masu aikin ceto Palasdinawa a Rafah da ke kudancin zirin Gaza, tare da bayyana hakan da aikata laifukan yaki.

Sojojin Isra’ila sun amince a ranar Asabar 29 ga watan Maris cewa sun yi luguden wuta kan motocin daukar marasa lafiya a zirin Gaza, inda Hamas ta yi Allah wadai da harin” da ya janyo asarar rayukan ma’aikatan ceto.

Rahotanni sun ce an gano gawarwakin ma’aikatan ceto goma sha biyar, wadanda aka binne a kusa da motocinsu, wadanda suka lalace gaba daya sakamakon harin na Isra’ila.

Har ila yau kungiyar ta jaddada cewa kai hare-hare da gangan kan masu kai agajin da suke gudanar da ayyukansu na jin kai na nuni da daya daga cikin manyan laifukan keta dokokin yaki kuma wani bangare ne na hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da kaiwa kan fararen hula a zirin Gaza.

Hamas ta kuma yi Allah wadai da shirun da kasashen duniya suka yi wajen fuskantar irin wadannan laifuffuka, tana mai cewa rashin daukar matakin wani abu ne da ba za a amince da shi ba.

Ma’aikatar lafiya ta gwamnatin Hamas a zirin Gaza ta fada a yau asabar cewa mutane 921 ne suka mutu a yankin tun bayan da Isra’ila ta sake kai hare-hare a ranar 18 ga Maris, ciki har da 25 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muna so a nuna wa duniya mutanen da suka kashe ’yan Arewa a Edo — Gwamnan Kano
  • Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka
  • Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano
  • Somalia: Harin Amurka a kan kungiyar IS ya kashe wasu mambobin kungiyar
  • Hamas ta yi Tir da kakkausar murya da harin Isra’ila kan masu aikin ceto a Gaza
  • Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar
  • Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo
  •  Iran Ta Yi Allawadai Da Sabon Harin HKI A Kasar Lebanon
  • An cafke mutum 19 bayan arangama tsakanin sojoji da ’yan shi’a a Abuja