Maduro Ya Bayyana Sakataren Harkokin Wajen Amurka Da Cewa Wawa Ne
Published: 29th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne.
A yayin ziyarar da sakataren na harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan har ta kai wa Guyanan hari.
Rubio ya kara da cewa; Idan haka ta faru, to kuwa Venezuela za ta gwammace kida da karatu a wannan rana.
Amurkan dai ta kulla yarjejeniyar tsaro da kasar ta Guyana a yayin ziyarar da Rubio ya kai.
Shi kuwa shugaban kasar ta Venezuela da yake mayar da martani ya ce; Marco Rubio wawa, ya zo yana yi wa kasar Venezuela barazana daga kasar Guyana, sannan ya kara da cewa; Venezuela ta fi karfin a yi mata barazana, domin ita kasa ce ta ‘yanci.”
Alaka a tsakanin Venezuela ta Amurka ta sake tabarbarewa tun bayan da shugaba Donald Trump ya hau karagar mulki, bayan da ya kara kakaba mata takunkumai, da kuma batun mayar da ‘yan hijirar kasar daga Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Watsi Da Barazanar HKI
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da barazanar HKI na kaiwa cibiyoyin makamashin nukliyar kasar don hana kasar abinda take kira makaman Nukliya.
Ministan ya kara da cewa kasar Iran zata iya kare kanta ko da Amurka ce ta takaleta, kuma Amurka ta san hakan. Sannan ya ce HKI bata taba kaiwa Iran hari a bay aba kuma ba zata taba kai mata hari ba.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya buga wannan labarin a jiya Asabar ya kuma nakalto ministan yana cewa kasashen Rasha da Iran basu taba karfafa dangantakar tsakaninsu fiye da yanzu ba.
Aragchi ya kara da cewa kasashen Iran Rasha da kuma China suna aiki tare don tabbatar da zaman lafiya a duniya a cikin yan shekarun da suka gabata. Kuma kasashen da gaske suke a kan hakan.