Kisan ‘Yan Arewa 16 A Jihar Edo: Gidauniyar Sir Ahmadu Bello Ta Nemi Adalci
Published: 29th, March 2025 GMT
Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta yi ala wadai da kisan gilla da aka yi wa ‘yan Arewa 16 a Uromi, Jihar Edo, a ranar 28 ga Maris, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda abin ya shafa suna kan hanyarsu daga Fatakwal zuwa Kano lokacin da aka kai musu farmaki, aka sare su, sannan aka banka musu wuta a abin da gidauniyar ta bayyana a matsayin abin “aikin rashin imani” na tashin hankali bisa la’akari da bambancin kabilanci.
A cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na gidauniyar, Injiniya Dakta Abubakar Gambo Umar, ya fitar, gidauniyar ta nuna damuwarta kan yadda hare-haren da ake kai wa ‘yan Arewa ke ƙaruwa a wasu sassan Kudancin kasan nan, tana gargaɗin cewa irin waɗannan munanan ayyukan na barazana ga hadin kan kasa da zaman lafiya.
“Muna matuƙar ƙin wannan aika-aika da aka yi wa ‘yan Najeriya bisa la’akari da kabilanci da yankuna,” in ji sanarwar.
“Abin baƙin ciki ne cewa ‘yan ƙasa ba za su iya yin tafiye-tafiye cikin kasarsu ba cikin tsaro da kwanciyar hankali, ba tare da fargabar farmaki ko cutarwa ba.”
Gidauniyar ta tuna da wasu hare-haren da aka kai a baya kan ‘yan Arewa a Kudancin kasan nan.
“Ba zamu manta da kisan ‘yan Arewa uku a Jihar Anambra a ranar 18 ga Janairu, 2022 ba, da kisan direbobin tirela biyu a Jihar Enugu a ranar 14 ga Yuli, 2023, inda aka kona motocinsu, da kuma kisan ‘yan Arewa biyar a Jihar Delta a ranar 30 ga Oktoba, 2024,” sanarwar ta karanta.
“Kuma ba za mu manta da kisan gillar da aka yi wa wata mace mai ciki, Harira Jibril, da ‘ya’yanta mata guda huɗu a Jihar Ebonyi a ranar 23 ga watan Mayun 2021 ba.”
“Waɗannan abubuwa da makamantansu sun nuna wani yanayi mai tayar da hankali da bai kamata a yi shiru a kansa ba,” in ji gidauniyar.
Gidauniyar Sir Ahmadu Bello Memorial ta buƙaci a gaggauta kama tare da gurfanar da masu hannu a kisan Uromi, tare da biyan diyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa.
“Muna buƙatar adalci cikin gaggawa, dole ne hukumomi su hukunta waɗanda suka aikata wannan ta’asa,” sanarwar ta ci gaba.
Haka kuma, gidauniyar ta roƙi shugabannin Kudancin kasan nan su ɗauki matakan wayar da kan al’ummominsu don gujewa ɗora laifi bisa la’akari da kabilanci da aikata ayyukan tashin hankali.
“Ba kowa ne ke da ikon ɗaukar doka a hannunsa ba,” in ji ta.
“Allah wadai kadai ba ya isa; dole ne a yi adalci.”
Sanarwar ta jaddada cewa kowanne ɗan Najeriya na da ‘yancin rayuwa da aiki a kowane yanki na ƙasa, tana mai buƙatar gwamnati da ta tabbatar da kariya ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.
“Idan ba mu magance irin waɗannan hare-haren ba, muna fuskantar barazanar ramuwar gayya da rarrabuwar ƙasa,” gidauniyar ta yi gargaɗi.
“Don ƙasarmu ta ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya, haɗin kai da jituwa, dole ne mu yi watsi da duk wani nau’in nuna wariya da tashin hankali.”
Wannan lamari ya haifar da gagarumar fusata a fadin ƙasa, tare da kiran ga gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen rikicin kabilanci da tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.
Rel: Khadija Kubau
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Arewa Edo Gidauniyar Jihar Yan
এছাড়াও পড়ুন:
Zaɓen 2027: Babu ɗan takarar da zai yi nasara ba tare da goyon bayan Arewa ba — Hakeem
Tsohon mashawarcin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewacin ƙasar ba.
Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf.
NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari?Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba yankin Arewacin Nijeriya zai fuskanci alƙiblarsa ta siyasa.
“Nan da watanni shida mutanen Arewacin Nijeriya za su fayyace inda suka dosa, saboda haka zaɓi ya rage wa mutanen sauran yankunan ƙasar.
“Sai dai abin da muka sani ƙarara shi ne babu wanda zai zama shugaban Nijeriya ba tare da goyon bayan Arewa ba.
Ya bayyana damuwa kan yanayin da aka tsinci kai a ƙasar a halin yanzu, inda ya buƙaci ’yan Arewa da su guji faɗa wa tarkon ’yan siyasa mayaudara a zaɓen da ke tafe.
“Muna so a samu gwamnatin da ta fahimci matsalolinmu kuma wadda za ta iya magance su.
“Bayan shekaru takwas da Buhari ya yi a karagar mulki mun ƙara buɗe ido. A yanzu wata gwamnatin ce amma har yanzu kuka muke yi. Shikenan kullum a kuka za mu ƙare?
Kazalika, Baba-Ahmed ya bayyana yadda yankin Arewa ya tagayyara a sakamakon rikicin Boko Haram wanda ya taɓa duk mabiya addinai, lamarin da ya jaddada muhimmancin haɗin kai.
“Mun dawo daga rakiyar yaudarar da ake yi mana ta zaɓen ɗan takara saboda ƙabilanci ko addini. Yanzu an rufe wannan babi.
“Yanzu abin da kawai muke buƙata shi ne shugaba nagari wanda zai magance matsalolin da muke fama da su,” in ji shi.