Gwamnatin HKI ta bukaci hukumar hukumar ayyukan leken asiri na kasar MOSAD ta nemi kasashe musamman a nahiyar Afirka wadanda zasu amince su karbi Falasdinawan da za’a kora daga Gaza.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyoyin HKI na cewa Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu yana neman wata kasa ko kasashen nesa da HKI da dukkan kilomita don maida mutanen kaza zuwa can.

Wasu ma’aikatan MOSAD biyu, da kuma wani jami’in gwamnatin Amurka sun fadawa shafin labarai na yanar gizo Axios, kan cewa tun sun rika sun tattauna da kasashe Somalia da Sudan ta kudu da kasar Indonasia da wasu da dama dangane da wannan batun.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin HKI ta kashe fiye da mutanen 50,000 a Gaza sannan ta kori wasu daga yankin.

Sannan a halin yanzu an tarwatsa kashi 90 daga cikinsu, a cikin zirin na gaza, wanda zai basu damar kamasu da kuma maida su duk inda suek so a duniya da karfi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu

Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia.

Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da  kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda  lamarin ya shafa.

Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu.

“Kamar yadda aka bayyana a ranar Laraba 26 ga watan Maris 2025, jimillar kuɗin da aka tattara sun kai Naira miliyan 839. Bisa ga kididdiga da aka yi, kowanne daga cikin mutanen da lamarin ya shafa kai tsaye zai karɓi kimanin Naira miliyan huɗu.

“Ga waɗanda suka rasu, za a ba da kuɗin ga iyayensu ko magadansu, yayin da waɗanda suka tsira za su karɓi nasu da kansu.

“Kayan tallafin da aka riga aka tara, musamman abinci da sauran kayayyakin bukata, tuni an raba su ga waɗanda suka shafi lamarin“, in ji shi.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa akalla mutane 210 ne lamarin ya ritsa da su, inda 100 daga cikinsu suka mutu nan take.

“An tabbatar da cewa mutane 33 daga cikin waɗanda suka rasu magidanta ne, kuma 31 daga cikinsu sun bar ‘yaya. Jimillar matan da suka rasa mazajensu sakamakon lamarin sun kai 42, yayin da yaran da suka zama marayu suka kai 133″, in ji Gwamna Namadi.

A yayin jajantawa ga waɗanda lamarin ya shafa, Gwamnan ya yi kira ga direbobin manyan motocin dakon mai da sauran masu amfani da tituna su kasance masu taka tsantsan domin gujewa sake afkuwar irin wannan mummunan lamari.

“Iftila’in da ya afku a Majia ya koyar da mu darussa masu yawa, wanda muke fatan jama’a da masu ruwa da tsaki, musamman ma waɗanda ke harkar sufuri, za su dauki darasi“. Inji shi.

Gwamnan ya kuma shawarci waɗanda suka karɓi tallafin su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata, musamman wajen kafa sana’o’i.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gaza : Fiye da mutane 1,000 Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga Maris
  • Wani Asbiti A Amurka Ya Kori Wata Likita Daga Aiki Bayan Ta Yi Allawadai Da Yahudawan Sahyoniyya
  • Ƴansanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ɗan Bijilanti A Tawagar Sarki Sunusi II
  • Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano
  • Miji ya kama matarsa da kwarto ta na’urar drone
  • Hamas A Gaza Ta Amince Da Kafa Gwamnatin Hadin Kan Falasdinawa, Amma Makamanta Jan Layi Ne
  • Karamar Hukumar Jahun Ta Karrama Hakimai Da Limamai Da Kayan Sallah
  • Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu
  • Mai Bawa Jagora Shawara Ya Ce ‘Wa’adussadik Na III” Na Kan HKI Na Hanya