Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo
Published: 29th, March 2025 GMT
’Yan Sanda sun kama mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan matafiya 16 ’yan Arewa a kan titin Uromi zuwa Obajana, a Jihar Edo.
Sufeto-Janar na ’Yan Sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya yi tir da wannan hari, kuma ya bai wa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Hedikwatar Rundunar da ke Abuja, yin bincike.
Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 1,800 aiki An cafke mutum 19 bayan arangama tsakanin sojoji da ’yan shi’a a AbujaBayan faruwar lamarin, rundunar ’yan sandan Jihar Edo, ta tura jami’anta zuwa yankin domin wanzar da zaman lafiya.
Har ila yau, ana ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere.
Kakakin rundunar ’yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce Sufeto-Janar ya ba da umarnin a kamo waɗanda ke da hannu a lamarin.
Ya tabbatarwa da al’umma cewa ’yan sanda ba za su yarda da kisan gilla ba, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.
Sufeto-Janar ya buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu kuma su ba da haɗin kai wajen bincike.
Haka kuma, ya gargaɗi mutane kan ɗaukar doka a hannunsu, tare da tunatar da su cewa mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba laifi ne.
’Yan sanda sun kuma gargaɗi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da kiran su da su riƙa kai rahoton duk wani abu da suka gani wanda ba su yarda da shi ga hukumomin tsaro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Matafiya Yan Arewa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kasar Guinea Ta Yi Wa Musa Dadis Camara Afuwa
Shugaban gwamnatin soja na kasar Guinea Janar Mamadi Doumbouya ne ya yi wa tsohon shugaban sojan kasar Camara afuwa bayan da aka yanke masa zaman gidan kurkuku bisa laifin kisan kiyashin da ya faru a 2009 a birnin Conakry.
Kafafen watsa labarun kasar ta Guinea ne su ka sanar da afuwar da shugaba Mamadi ya yi wa Camara bisa dalilai na rashin lafiya.
Bugu da kari kakakin fadar shugaban kasa Janar Amara Camara wanda ya yi sanarwar ya ce, an yi hakan ne bisa shawarar da ma’aikatar shari’a ta gabatar.
Camara dai ya mulki kasar ta Guinea ne daga 2008-2009, an kuma yi masa shari’a ne a watan Yuli na 2024, saboda yadda a zamanin mulkin nashi aka yi amfani da karfi wajen murkushe ‘yan hamayya da su ka yi wani taro a cikin filin wasan kwallon kafa.
Fiye da mutane 150 ne dai su ka kwanta dama, kuma jami’an tsaron kasar su ka yi wa mata fiye da 100 fyade.
Shari’ar da aka yi wa Camara wacce ta sami cikakken goyon bayan MDD, ta same shi da lafin gajiyawa wajen hukunta masu laifi.
Matakin na gwamantin yanzu ya biyo bayan shirinta na biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe da kuma yi wa illa.
Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama a kasar suna sa alamun tambaya akan wannan matakin na yi wa adalci Karen tsaye.