Aminiya:
2025-03-31@22:58:34 GMT

Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar

Published: 29th, March 2025 GMT

Gwamnatin Soji ta Myanmar, ta bayyana cewa mutum 1,002 sun rasa rayukansu sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta auku a ranar Juma’a.

Sama da mutum 2,000 sun jikkata, kuma ana ci gaba da ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe.

Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo An kashe mutum 10 a wani sabon hari a Filato

Jami’an agaji sun ce girgizar ƙasar ta fi shafar birnin Mandalay, inda asibitoci suka cika maƙil da waɗanda suka jikkata.

Shugaban mulkin soji na Myanmar, ya nemi taimakon ƙasashen duniya, amma ana fargabar yaƙin basasa da ke ci gaba a ƙasar zai hana ayyukan jin-ƙai tafiya yadda ya kamata.

Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce Myanmar na cikin yaƙi tun shekaru huɗu da suka wuce, wanda ya haifar da zargin cewa dakarun soji na tsare ɗaruruwan mutane.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Girgizar kasa Gwamnatin Soji Mutuwa Myanmar

এছাড়াও পড়ুন:

Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu

Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia.

Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da  kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda  lamarin ya shafa.

Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu.

“Kamar yadda aka bayyana a ranar Laraba 26 ga watan Maris 2025, jimillar kuɗin da aka tattara sun kai Naira miliyan 839. Bisa ga kididdiga da aka yi, kowanne daga cikin mutanen da lamarin ya shafa kai tsaye zai karɓi kimanin Naira miliyan huɗu.

“Ga waɗanda suka rasu, za a ba da kuɗin ga iyayensu ko magadansu, yayin da waɗanda suka tsira za su karɓi nasu da kansu.

“Kayan tallafin da aka riga aka tara, musamman abinci da sauran kayayyakin bukata, tuni an raba su ga waɗanda suka shafi lamarin“, in ji shi.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa akalla mutane 210 ne lamarin ya ritsa da su, inda 100 daga cikinsu suka mutu nan take.

“An tabbatar da cewa mutane 33 daga cikin waɗanda suka rasu magidanta ne, kuma 31 daga cikinsu sun bar ‘yaya. Jimillar matan da suka rasa mazajensu sakamakon lamarin sun kai 42, yayin da yaran da suka zama marayu suka kai 133″, in ji Gwamna Namadi.

A yayin jajantawa ga waɗanda lamarin ya shafa, Gwamnan ya yi kira ga direbobin manyan motocin dakon mai da sauran masu amfani da tituna su kasance masu taka tsantsan domin gujewa sake afkuwar irin wannan mummunan lamari.

“Iftila’in da ya afku a Majia ya koyar da mu darussa masu yawa, wanda muke fatan jama’a da masu ruwa da tsaki, musamman ma waɗanda ke harkar sufuri, za su dauki darasi“. Inji shi.

Gwamnan ya kuma shawarci waɗanda suka karɓi tallafin su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata, musamman wajen kafa sana’o’i.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muna so a nuna wa duniya mutanen da suka kashe ’yan Arewa a Edo — Gwamnan Kano
  • Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka
  • Girgizar Kasa: Shugaban Kasar Myanmar Ya Mika Godiya Ga Tawagar Likitocin Yunnan Ta Kasar Sin
  • Shugaba Xi Ya Jajantawa Shugaban Myanmar Game Da Girgizar Kasar Da Ta Auku
  • Adadin mamata a girgizar kasar Myanmar ya ka 1,644
  • Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu
  • Gwamnati Ta Ba da Umarnin Tafiya Yi Wa Ƙasa Hidima Ga Duk Masu HND
  • Me Ya Sa Fina-finai Masu dogon Zango A Masana’antar kannywood ke Zama Cin kwan Makauniya?
  • An kashe mutum 10 a wani sabon hari a Filato