Rikici ya ɓarke bayan wata mata ta mari ɗan sanda a Saudiyya
Published: 29th, March 2025 GMT
Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin ɗaukar matakin da ya dace bisa doka.
Bidiyon, wanda ya bayyana a ranar Juma’a, ya nuna matar tare da wata ƙawarta suna tunkarar wajen da aka kange, inda jami’an tsaro suka hana su wucewa.
Sai dai matar ta fusata, tare da marin ɗan sandan, shi ma daga bisani ya rama kafin wasu su shiga tsakani.
Lamarin ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke ganin matar ta ci zarafin jami’in tsaron yayin da yake bakin aikinsa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: askar Ɗan Sanda mari Saudiyya
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Rahoton Hana Shettima Shiga Villa
Fadar Shugaban Ƙasa ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da irin waɗannan labaran ƙarya, tare da kira ga kafafen yaɗa labarai su riƙa tabbatar da gaskiya labari kafin wallafawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp