Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300.

 

A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da yunwa da kuma samar da abinci ga al’umma.

A cewar sa, karamar Hukumar ta ware wasu yankunan Sahara domin fara noman rani a karo na farko dan fadada harkar noma a kan Tudu.

 

Alhaji Jamilu Danmalam yace an zabi kauyen Tunubu dake mazabar Kanwa domin fara noman Rani.

Ya kara da cewar, wadanda suka anfana da tallafin za su ci moriyar kaso 60 cikin 100, yayin da zasu dawowa da gwamnati kaso arba’in kacal 40.

 

A nasa jawabin, jami’in kula da noman rani Malam Suraja Dahiru ya ce gwamnatin Jihar Jigawa ta bada umarnin baiwa matasa filin noma a kalla kadada 100 a kowacce karamar hukuma.

Ya yi nuni da cewar, shugaban karamar Hukumar Jahun ne kadai ya kara adadin filin noma zuwa dari uku.

 

Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, kayayyakin tallafin da aka raba sun hada da Injin ban ruwa da takin zamani buhu bakwai da irin shuka na shinkafa buhu daya da injin feshi da maganin kwari da sauran kayan aikin gona.

 

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Jahun Noman Rani

এছাড়াও পড়ুন:

Yau Lahadi Ce Take Salla A Kasashen Larabawa Da Dama

A kasar Jordan gwamnatin kasar ta bada sanarwan cewa a gobe Litinin ce za’a gudanar da bukukuwan sallah karama bayan azumun watan Ramadan na kwanaki 30.

Muftin kasar ta Jordan Ahmed Hasanat a lokacinda yake bada sanarwan a jiya Asabar yace, ranar Litinin 31 ga watan Maris, ita ce ranar Sallah daya ga watan shawwal shekara ta 1446 Kmariya.

Kasashen Saudia, Qatar, UAE, Kuwait, Bahrain, Yemen, da kuma Palestine sun bada sanarwan cewa yau Lahadi ce sallah karama a kasashensu. Sai kuma kasashen Oman, Siriya da sun bayyana cewa gobe litinin ne salla karama.

A tarayyar Najeriya ma, sultan Sa’ad Abubakar na sokoto ya bada sanarwan sallah a yau Lahadi.

Majalisar koli ta al-amuran musulunci a Najeriya, karkashun shugabancin sultan Sa’ad Abubakar III ne ya bada wannan sanarwan a jiya da yamma.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Za Ta Inganta Wuraren Tarihi Domin Nishadantarwa A Duk Jihohin Nijeriya 
  • Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya
  • Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah
  • Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah
  • Yau Lahadi Ce Take Salla A Kasashen Larabawa Da Dama
  • Karamar Hukumar Jahun Ta Karrama Hakimai Da Limamai Da Kayan Sallah
  • Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah
  • Kungiyar “White Helmets Ta” A Kasar Siriya Ta Rasha Tallafin Da Take Samu Daga USAID
  • Wike Ya Jinjina Wa Tinubu kan Bunkasa Ilimi Mai Zurfi