Rikici Ya Turnuke Jam’iyyar SDP A Yayin Da Aka Samu Shugabanni Bangare Biyu A Kogi
Published: 29th, March 2025 GMT
Rikicikin ya turnuke jam’iyyar SDP a yayin da aka samu shugabanni bangare biyu a Jihar Kogi, rikicin ya kunno kai ne bayan da wani bangare ya kaddamar da kwamitin gudanarwa a Lakwaja.
Taron da aka gudanar a sakateriyar jam’iyyar na jihar, an zabi tsohon shugaban sashi na APC, Hon. Ahmed Attah a matsayin sabon shubagaba, tare da Alhaji Idris Sofada a matsayin sabon sakatare na jam’iyyar a jihar.
Wakilai 3,890 ne daga kananan hukumomi 21 na jihar suka zabi shugabanni 21 na jam’iyyar. Sannan kuma jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) sun kasance a wannan wuri lokacin zaben.
A jawabinsa na farko, Attag ya yi alkawarin zai yi gaskiya da adalci tare da daga martabar jam’iyyar SDP don samun nasara a zabe a gaba.
Ya yaba wa jami’an INEC da kwamitin shirya zaben da kuma jami’an tsaro wurin tabbatar da nasarar wannan taron. Ya ce wannan ya nuna yadda SDP za ta yi nasara a zaben gwamna a 2028.
Sai dai kuma wani bangare da Moses Peter Oricha yake jagoranta ya yi watsi da zaben, inda ya bayyana shi a matsayin wanda bai inganta ba.
Oricha, wanda shugabancinsa zai kare a watan Afrilun 2026, ya zargi masu shirya zaben da karya doka da kuma kin bin hukuncin kotu kan wannan lamari.
“An sanar da ni cewa wasu mutane da suke kiran kansu ‘ya’yan SDP ne sun shirya babban taron jam’iyyar a jihar. Wannan abun dariya ne kuma babban laifi ne. Wadannan mutane ana daukar nauyinsu ne domin su kawo rudani a cikin jam’iyyarmu,” in ji Oricha.
Ya bukaci mutane da hukumomin tsaro da INEC su yi watsi da taron, sannan kuma ya dauke shi a matsayin wani kokari na tarwatsa jam’iyyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya musanta cewa akwai tsamin dangantaka tsakaninsa da Gwamnatin Sakkwato.
Ana iya tuna cewa bayan karɓar akalar jagoranci ne Gwamna Ahmed Aliyu ya yi wa Dokar Masarautar Sakkwato gyaran fuska tare da sauke wasu sarakunan gargajiya, lamarin da aka riƙa raɗe-raɗin wani yunƙuri ne tsige shi kansa Sarkin Musulmin.
Hotunan Sallar Idi daga sassan duniya Masar ta miƙa wa Hamas da Isra’ila tayin tsagaita wutaSai dai da yake jawabi a saƙonsa na barka da sallah, Sarkin Musulmi ya ce “ba wata rashin jituwa ko faɗa a tsakaninmu.
“Muna aiki tare a koyaushe. Aikinmu mu taimaka wa gwamnatin [Sakkwato] kan shirye-shiryen da ta ɗauko domin ciyar da jama’a gaba.”
Ya yi kira ga al’ummar musulmi da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a domin samun nasara wajen sauke nauyin jama’a da rataya a wuyansu.
Kazalika, Alhaji Sa’ad ya ce karantarwar addini da aka samu a watan Azumi mai albarka abu ne da ya kamata a riƙe a sanya cikin aiki.
“Mu ƙara ɗaure ɗamara kar mu koma gidan jiya wajen aikata saɓon Allah. Mu dage da yin ibada kar a ja baya. Sannan mu riƙa yi wa shugabanni addu’a.
“Ku kuma shugabanni ku ji tsoron Allah cikin jagoranci. Idan za a yi ayyukan jama’a kar a ji tsoron kowa sai Allah,” in ji Sarkin Musulmi.
Sarkin ya yi kira ga jami’an tsaro da su ktara ƙaimi wajen magance matsalar tsaro domin a cewarsa har yanzu akwai sauran aiki a ba iya Jigar Sakkwato kaɗai ba.