Hamas ta yi Tir da kakkausar murya da harin Isra’ila kan masu aikin ceto a Gaza
Published: 29th, March 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan kungiyoyin kare fararen hula da masu aikin ceto Palasdinawa a Rafah da ke kudancin zirin Gaza, tare da bayyana hakan da aikata laifukan yaki.
Sojojin Isra’ila sun amince a ranar Asabar 29 ga watan Maris cewa sun yi luguden wuta kan motocin daukar marasa lafiya a zirin Gaza, inda Hamas ta yi Allah wadai da harin” da ya janyo asarar rayukan ma’aikatan ceto.
Rahotanni sun ce an gano gawarwakin ma’aikatan ceto goma sha biyar, wadanda aka binne a kusa da motocinsu, wadanda suka lalace gaba daya sakamakon harin na Isra’ila.
Har ila yau kungiyar ta jaddada cewa kai hare-hare da gangan kan masu kai agajin da suke gudanar da ayyukansu na jin kai na nuni da daya daga cikin manyan laifukan keta dokokin yaki kuma wani bangare ne na hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da kaiwa kan fararen hula a zirin Gaza.
Hamas ta kuma yi Allah wadai da shirun da kasashen duniya suka yi wajen fuskantar irin wadannan laifuffuka, tana mai cewa rashin daukar matakin wani abu ne da ba za a amince da shi ba.
Ma’aikatar lafiya ta gwamnatin Hamas a zirin Gaza ta fada a yau asabar cewa mutane 921 ne suka mutu a yankin tun bayan da Isra’ila ta sake kai hare-hare a ranar 18 ga Maris, ciki har da 25 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojan HKI Ya Halaka A Gaza
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa sojansu daya ya halaka a Gaza yayin da wasu 4 su ka jikkata bayan da aka kai wa motar da take dauke da su mai sulke hari.
Majiyar ta kuma ce ana ci gaba da yin fada mai tsanani a tsakanin sojojin Isra’ilan da kuma ‘yan gwagwarmaya a yankunan daban-daban na zirin Gaza.
Majiyar Falasdinawa ta ce; ‘yan gwgawarmaya sun tarwatsa wata tankar yakin HKI ta hanyar tashin wani bom da aka ajiye a kan hanya.
An ga jiragen yakin HKI masu saukar angulu suna jigilar daukar wadanda su ka jikkata sanadiyyar harin.
A gefe daya, Falasdinawa da dama sun yi shahada a wasu hare-hare da ‘yan sahayoniya su ka kai akan yankin na Gaza. Tun da safiyar yau Asabar ne dai ‘yan sahayoniyar su ka rika kai hare-haren wanda ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 30.