Saudiyya ta sanar da hango watan Shawwal, ranar lahadi ce Sallah a kasar
Published: 29th, March 2025 GMT
Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da hango jinjirin watan Shawwal, wanda ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadana.
Shafin Haramain ne ya ruwaito hakan, bayan daukar awanni ana neman wata.
Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar karamar Sallah a kasar ta Saudiyya.
.উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
NUJ Kebbi Tayi Kiran Ayi Bukukuwan Sallah Lafiya
Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kebbi, NUJ, ta taya gwamnatin jihar da al’ummar musulmin jihar murnar zagayowar ranar Sallah.
Majalisar a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar da Sakatare, Ismail Adebayo, ta yi murna da al’ummar musulmin jihar kan kammala azumin kwanaki 29 na watan Ramadan da kuma bikin Eid-Fitr.
Ta yi kira da a zauna lafiya da juna a tsakanin al’ummar jihar bisa koyarwar addinin Musulunci da manzon Allah mai tsira da amincin Allah tare da la’akari da muhimmancin watan Ramadan da Idi-El-Fitr.
Majalisar ta yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Nasir Idris kan kayayyakin abinci da aka rabawa musulmi a cikin watan azumin Ramadan.
Ta yi kira ga al’ummar jihar da su marawa gwamnati baya a ayyuka daban-daban da ta fara don bunkasa tattalin arzikin jihar da al’ummarta tare da yi musu fatan bukukuwan Sallah lafiya.
PR/Abdullahi Tukur