Gobe take Sallah a Nijeriya — Sarkin Musulmi
Published: 30th, March 2025 GMT
An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana.
Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi.
Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya Ramadan Shawwal
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Jahun Ta Karrama Hakimai Da Limamai Da Kayan Sallah
Shugaban Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam ya kaddamar da rabon kayan sallah da kuma kudin dinki ga al’ummar yankin.
A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a garin Jahun, shugaban Karamar Hukumar yace Hakimai na gundumomin Jahun da Aujara da Gunka da Kadawawa da Limaman masalatan juma’a 79 na yankin za su amfana da kayan sallah da kuma kudin dinki.
Jamilu Muhammad Danmalam ya bayyana rashin Jin dadinsa bisa yadda ake mantawa da iyayen kasa da Malaman Addini a irin wannan lokacin da ya kamata a taimake su.
Ya ce yana daya daga cikin kudurorinsa na shigo da kowanne bangare na al’umma cikin tsarin shugabancinsa dan kowa ya anfana.
Danmalam ya ce a wannan wata na Ramadan karamar hukumar ta tallafawa masu bukata ta musamman da marayu da masu karamin karfi da shugabannin jam’iyyar APC da ma’aikatan gwamnati da kuma mata da maza.
Ya kara da cewar kowanne hakimi ya sami dinkin sallah na shadda mai dauke da shakwara da jamfa da wando, hade da kudin abincin sallah.
A jawabin sa, daya daga cikin limaman yankin Mallam Yahuza Gabari yace a tarihin Karamar Hukumar Jahun ba’a taba samun shugaban da ya kula da limamai da shugabannin al’umma irin shugaban Karamar Hukumar na yanzu ba.
Wasu daga cikin wadanda suka anfana da tallafin sun yabawa shugaban Karamar Hukumar bisa tagomashin da suka samu.
Usman Mohammed Zaria