Sin Da Jamhuriyar Congo Za Su Karfafa Raya Hadin Gwiwar Sin Da Afrika
Published: 30th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na Janhuriyar Congo Jean-Claude Gakosso, jiya Juma’a a birnin Beijing, inda suka yi alkawarin hada hannu wajen inganta raya dangantakar Sin da Afrika.
Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya ce dangantakar dake tsakanin Sin da Janhuriyar Congo, ta zama misalin hadin gwiwa da goyon baya dake tsakanin Sin da Afrika.
Wang Yi ya kuma yi kira ga kasashen Sin da Afrika da su hada kai da kara hadin gwiwa domin kare muradun kasashe masu tasowa, da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a duniya yayin da ake fuskantar hargitsi.
A nasa bangare, Jean-Claude Gakosso, ya ce Janhuriyar Congo na daukar matsayinta na daya daga ci shugabannin dandalin FOCAC da muhimmanci, kuma a shirye take ta hada hannu da kasar Sin wajen shirya taron ministoci masu aiwatar da sakamakon taron FOCAC, da baje kolin cinikayya da tattalin arziki na Sin da Afrika, da kuma kara samar da sakamako daga hadin gwiwar Sin da Afrika. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sirrin da ke Tattare da Ganyen Mangwaro Ga Lafiyar Ɗan Adam
Wannan hanya, na matukar taimakawa sosai wajen sarrafa sinadarin insulin a jikin mutum.
2-Maganin Hawan Jini (Hypertension)
Ganyen mangwaro na rage matsin jini, sannan kuma yana karfafa jijiyoyin jini.
Saboda haka, a nan sai a nemi sabbin ganyen mangwaro, a tafasa su sosai a tace, sannan a sha rabin kofi da safe da kuma yamma.
3-Maganin Basir Sadidan
Idan ana fama da basir, za a iya amfani da ganyen mangwaro don rage kumburi da ciwo.
Bayan an samu wannan ganye na mangwaro, sai a busar da shi a kuma daka shi har sai ya zama gari. kana sai a dauki cokali daya na garin a hada da rabin kofi na ruwan dumi, sannan a zuba zuma a ciki kadan a sha kullum har sai an samu sauki.
4-Maganin Cututtukan da ke Cikin Baki
Idan ana fama da kuraje a baki, zubar jini daga hakora ko kuraje a harshe, ganyen mangoro na da matukar amfani wajen magance su.
A nan, tafasa ganyen za a yi a tace, sannan a yi amfani da ruwan wajen wanke baki sau uku a rana. Idan ana so kuma za a iya kara gishiri dan kadan, don karin karfi.
5-Maganin kunar Wuta
Idan aka samu kuna, ganyen mangoro na taimakawa wajen rage radadi da saurin warkewa.
Saboda haka, sai a busar da ganyen, a kone shi har sai ya zama toka. Sai a yi amfani da tokar wajen shafawa a wurin da aka konen.
6-Maganin Cututtukan da Suka Shafi Ciki
Ganyen mangwaro na taimakawa wajen magance matsalolin ciki, kamar ciwon ciki da kuma gudawa.
A nan za a tafasa ganyen ne, sannan a rika shan ruwan kullum sannu a hankali.
7-Rage Zafin Jiki da Rashin Nutsuwa (Stress & Andiety)
Idan ana fama da zafin jiki ko rashin hutu, ganyen mangwaro na taimakawa kwarai da gaske wajen kawar da su.
Za a tafasa shi, sannan a rika shan ruwan ko kuma a rika yin wanka da shi, domin samun nutsuwa.
8-Maganin Cututtukan Huhu (Tari, Mura da Sanyi)
Ganyen mangwaro na taimakawa wajen maganin tari, mura da kuma sanyi.
Ana tafasa shi a sha ruwan, domin rage tari da samun waraka daga cutar mura da kuma ta sanyi.
9-Inganta Lafiyar Mahaifa da Haihuwa
Ganyen mangwaro na da matukar amfani ga mata masu fama da matsalolin mahaifa.
Har ila yau, yana taimakawa wajen tsaftace mahaifa da kuma kara samun damar haihuwa.
don haka, a nan sai a tafasa ganyen a tace shi, sannan a rika shan sa da dumi.
10-Maganin Makakin Makogwaro da Ciwon Wuya
Idan ana fama da kuraje a makogwaro ko ciwon wuya ko kuma makaki, ganyen mangwaro na taimakawa kwarai da gaske wajen warkar da su.
Saboda haka, sai a tafasa shi sosai a yi amfani da ruwan ta hanyar kurkurawa da safe da kuma yamma.
Bugu da kari, ganyen mangwaro na da matukar amfani ga lafiyar jikin dan’adam. Idan ana son cin gajiyar fa’idarsa yadda ya kamata, yana da kyau a rika amfani da shi akai-akai.
Sannan, duk da haka; yana da matukar kyau a nemi shawarar likita kafin
a fara amfani da kowane irin maganin gargajiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp