Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Fiji: Ya Kamata A Koyi Fasahohin Da Kasar Sin Ta Samu A Fannin Raya Kasa
Published: 30th, March 2025 GMT
Shugaban majalisar dokokin kasar Fiji Filimone Jitoko, ya ce yadda kasar Sin ta samar da nagartattun manufofi, da samun nasarar kawar da fatara, da inganta tsarin dimokradiyya, ta yadda za ta shafi dukkan bangarorin zaman al’umma, sun kasance abin koyi ga kasarsa.
Filimone Jitoko, ya bayyana hakan ne kwanan nan yayin zantawarsa da wata wakiliyar CMG a birnin Beijing, lokacin da ya ziyarci kasar Sin a karon farko, inda ya ce ziyarar ta ba shi damar samun karin ilimi, da kuma yin tunani mai zurfi.
Ya kara da cewa, kasar Fiji na godiya ga kasar Sin bisa yadda take fahimtar bukatun kananan tsibiran dake yankin tekun Pasifik ta fuskar tinkarar sauyin yanayi, kuma Fiji na fatan zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni da dama, kamar na aikin gona, da kamun kifi, da kayayyakin more rayuwa, da gina hanyoyi, da dai sauransu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ana Share Fagen Gudanar Bikin Baje Kolin Kayayyakin Da Ake Shigar Da Su Kasar Sin Yadda Ya Kamata
A yau Litinin, hukuma mai kula da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare, ta bayyana cewa, yanzu haka ana share fagen gudanar da bikin yadda ya kamata, inda yawan fadin shagunan da kamfanoni daban-daban suka kulla kwangilolin baje kolin kayayyakinsu a ciki ya kai muraba’in mita dubu 240, kuma ya kai 2/3 na fadin wurin da aka tanada.
Bikin nan da za a gudanar da shi a karo na 8, zai samu ci gaba a bangarori hudu. Na farko, za a tabbatar da fadin wurin bikin da ya kai muraba’in mita dubu 360, don baje kolin kayayyakin zamani. Na biyu, za a samar da dandaloli masu kyau ga mu’ammalar jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa don kara hadin gwiwarsu. Na uku kuma akwai batun taimakawa matsakaita da kananan kamfanoni wajen kafa karin shirin tattalin arziki na yanar gizo, da makamashi masu tsafta da sauransu. Na hudu kuma, za a kara kokarin tabbatar da ingancin kayayyakin da ake shigar da su, da gayyatar karin kamfanoni a matakai daban-daban da su halarci bikin, ta yadda za a gaggauta samun daidaito tsakanin bukatun dake akwai da bangaren samar da kayayyaki. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp