Karamar Hukumar Jahun Ta Karrama Hakimai Da Limamai Da Kayan Sallah
Published: 30th, March 2025 GMT
Shugaban Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam ya kaddamar da rabon kayan sallah da kuma kudin dinki ga al’ummar yankin.
A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a garin Jahun, shugaban Karamar Hukumar yace Hakimai na gundumomin Jahun da Aujara da Gunka da Kadawawa da Limaman masalatan juma’a 79 na yankin za su amfana da kayan sallah da kuma kudin dinki.
Jamilu Muhammad Danmalam ya bayyana rashin Jin dadinsa bisa yadda ake mantawa da iyayen kasa da Malaman Addini a irin wannan lokacin da ya kamata a taimake su.
Ya ce yana daya daga cikin kudurorinsa na shigo da kowanne bangare na al’umma cikin tsarin shugabancinsa dan kowa ya anfana.
Danmalam ya ce a wannan wata na Ramadan karamar hukumar ta tallafawa masu bukata ta musamman da marayu da masu karamin karfi da shugabannin jam’iyyar APC da ma’aikatan gwamnati da kuma mata da maza.
Ya kara da cewar kowanne hakimi ya sami dinkin sallah na shadda mai dauke da shakwara da jamfa da wando, hade da kudin abincin sallah.
A jawabin sa, daya daga cikin limaman yankin Mallam Yahuza Gabari yace a tarihin Karamar Hukumar Jahun ba’a taba samun shugaban da ya kula da limamai da shugabannin al’umma irin shugaban Karamar Hukumar na yanzu ba.
Wasu daga cikin wadanda suka anfana da tallafin sun yabawa shugaban Karamar Hukumar bisa tagomashin da suka samu.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Kayan Sallah shugaban Karamar Hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya
Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal, wanda ke nuna ƙarshen azumin watan Ramadan na bana.
Kwamitin duban wata na ƙasar ya bayyana cewa an ga jinjirin wata a yammacin yau, wanda ke tabbatar da cewa gobe za a fara bukukuwan Sallah.
Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge MijinkiWannan na nufin cewa al’ummar Musulmi a Saudiyya za su yi bikin ƙaramar Sallah, domin kammala azumin da suka gudanar a tsawon watan Ramadan.
Hukumomi sun buƙaci jama’a da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da bin dokoki don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp