Kamfanin hakar ma’adinai mai suna RUSAL na kasar Rasha ya aika da tawaga zuwa kasar Saloyo a yammacin Afirka don nazarin yiyuwar fara hakar ma’adinin bauxite a kasar nan gaba.

Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya nakalto jakadan kasar Rasah a Saliyo yana fadar haka.

Labarin ya nakalto Mohammad Yongawo wani jami’in gwamnatin kasar ta Saliyo yana cewa kasarsa a shirye take ta kammala yarjeniya tsakanin kamfanin Rusal na kasar Rasha don fara aiki a yankunan da ske da ma’adinin bauxite.

Ya kuma kara da cewa a halin yanzun bangarorin biyu suna cikin tattaunawa a tsakanionsu. Sannan yana fatan daga karshen gwamnatin kasar zata bawa kamfanin lisisin fara hakar ma’anin a kasar nan ba da dadewa ba.

Kafin haka dai ministan ma’adinai na kasar ta Saliyu Julius Mattai ya fadawa kamfanin dillancin labaran Sputnik kan cewa an fara tattaunawa tsakanin gwamnatinsa da kamfanin a birnin Free Town.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Rasha

এছাড়াও পড়ুন:

Wani Jami’in Leken Asirin HKI Ya Bukaci Kasashen Afirka Su Taimaka Su Karmi Falasdinawan Da Za;a Kora Daga Gaza

Gwamnatin HKI ta bukaci hukumar hukumar ayyukan leken asiri na kasar MOSAD ta nemi kasashe musamman a nahiyar Afirka wadanda zasu amince su karbi Falasdinawan da za’a kora daga Gaza.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyoyin HKI na cewa Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu yana neman wata kasa ko kasashen nesa da HKI da dukkan kilomita don maida mutanen kaza zuwa can.

Wasu ma’aikatan MOSAD biyu, da kuma wani jami’in gwamnatin Amurka sun fadawa shafin labarai na yanar gizo Axios, kan cewa tun sun rika sun tattauna da kasashe Somalia da Sudan ta kudu da kasar Indonasia da wasu da dama dangane da wannan batun.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin HKI ta kashe fiye da mutanen 50,000 a Gaza sannan ta kori wasu daga yankin.

Sannan a halin yanzu an tarwatsa kashi 90 daga cikinsu, a cikin zirin na gaza, wanda zai basu damar kamasu da kuma maida su duk inda suek so a duniya da karfi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Gano Babban Yankin Hakar Danyen Mai A Tekun Kudancin Kasar
  • Jakadan Kasar Sin Ya Bukaci Hadin Gwiwar Inganta Amfani Da AI Don Amfanar Da Kowa
  • An Fara Yakin Neman Zabe A Kasar Gabon
  • Wani Asbiti A Amurka Ya Kori Wata Likita Daga Aiki Bayan Ta Yi Allawadai Da Yahudawan Sahyoniyya
  • Iran: Amurka ta hada kai da Isra’ila wajen kawo cikas ga harkar tsaro a gabas ta tsakiya
  • Siriya : Ofishin jakadancin Amurka ya yi gargadi game da yiyuwar hare-hare a yayin bikin sallah
  • Mai Bawa Jagora Shawara Ya Ce ‘Wa’adussadik Na III” Na Kan HKI Na Hanya
  • Wani Jami’in Leken Asirin HKI Ya Bukaci Kasashen Afirka Su Taimaka Su Karmi Falasdinawan Da Za;a Kora Daga Gaza
  • Kungiyar “White Helmets Ta” A Kasar Siriya Ta Rasha Tallafin Da Take Samu Daga USAID