Hamas A Gaza Ta Amince Da Kafa Gwamnatin Hadin Kan Falasdinawa, Amma Makamanta Jan Layi Ne
Published: 30th, March 2025 GMT
Kungiyar Hamasa a gaza ta bada sanarwan cewa ta amince da shawarar da kasashen da suke shiga tskaninta da HKI kan cewa ta amince da kafa gwamnatin hadin kan Falasdinawa, amma ba zata taba mika makamanta ga wani ba ko waye shi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban Kungiyar Khalil Al-Hayya yana fadar haka a jiya Asabar a wani jawabin da ya gabatar da faifen bidiyo.
Al-Hayya ya kara da cewa muna karban dukkan shawarori masu ma’ana idan an bijirosu gare mua. Amma batun makamanmu, ba zamu taba kyale mutanemmu a hannun yahudawan sahyoniyya ko kuma wasu shuwagabannin Falasdinawa wadanda zasu mika su ga yahudawa ba suna ta yawo da hanka;linsu ba.
Yace fatammu ne gwamnatin HKI ba zata hana zabe gudana a kasar Falasdinu da kuma kafa gwamnatin Falasdinawa a gaza da yankin yamma da kogin Jordan sannan birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka : Ana ci gaba da zanga-zangar kyamar tsare -tsare da manufofin gwamnatin Trump
Ana sake gudanar da manyan zanga-zanga a manyan biranen Amurka a kan nuna adawa da tsare -tsare da manufofin gwamnatin Donald Trump.
Masu zanga-zangar na zargin gwamnatin da keta haddin kundin tsarin mulki da ‘yancin jama’a.
Wannan shi ne karo na biyu a wannan wata da dubban mutane suka yi tattaki a titunan Amurka domin nuna bacin ransu kan yadda Trump ke gudanar da mulkin kasar.
Korafe-korafen masu zanga-zangar sun hada da korar baki daga kasar da korar ma’aikata da gwamnati ke yi da kuma zargin tauye ‘yancin fadin albarkacin baki.
Kazalika masu zanga-zangar na nuna fishi kan irin ikon da Trump ya bai wa Elon Musk, attajirin duniya mai kamfanin Tesla – wanda ya kori ma’aikatan gwamnati sama da dubu 200, ya kuma rushe hukumomin agaji na Amurka da dama a duniya.