Aminiya:
2025-04-01@11:00:04 GMT

Masar ta miƙa wa Hamas da Isra’ila tayin yarjejeniyar tsagaita wuta

Published: 30th, March 2025 GMT

Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, tana mai cewa za ta yi amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra’ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50.

Babban jami’in Hamas da baya zaune a Gaza, Khalil al-Hayyam, ya ce ƙungiyar ta amince da ƙudirin da masu shiga tsakani daga Masar da kuma Qatar suka gabatar.

Miji ya kama matarsa da kwarto ta na’urar drone Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah

Ofishin firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ma ya ce ya karɓi tayin, amma ya gabatar da nasa tayin ”wanda ya ci karo da wanda masu shiga tsakanin suka gabatar masa, a ƙarƙashin jagorancin Amurka.”

BBC ya ruwaito cewa idan har ya tabbata, sabon shirin tsagaita wutar ya zo daidai da bakin ƙaramar Sallah da musulmai suka fara a ranar Lahadi.

A ranar Asabar, ofishin Nethanyahu ya ce ya yi zaman tuntuɓa game da sabon tayin da masu shiga tsakani suka gabatar masa.

Ya kuma ce ya gabatar da nasa sharaɗin, wanda Amurka ta yi amanna da shi, duk da cewa ofishin bai yi ƙarin bayani a kai ba. Itama Amurka ba ta kai ga cewa komai ba a kai kawo yanzu.

Wannan na zuwa ne yayin da dakarun Isra’ila suka ƙaddamar da sabbin hare-hare a Rafah da sassan Gaza bayan ƙarewar wa’adin tsagaita wutar da aka ƙulla a ranar 19 ga watan Janairu tsakanin ɓangarorin.

Tun bayan ƙarewar wa’adin har yanzu ɓangarorin sun gaza amincewa da fara aiwatar da zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar.

A zangon farko na yarjejeniyar tsagaita wutar dai Hamas ta saki ƴan Isra’ila 33, kuma har yanzu tana ci gaba da riƙon wasu 59, duk da dai ana zaton wasu daga cikin su sun mutu.

A baya dai Hamas ta haƙiƙance kan aiwatar da yarjejeniyar a yadda take tun farko, da kuma tattauna zango na biyu wanda zai kai ta ga sakin sauran mutanen da ta yi garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya ta hanyar janyewar dakarun Isra’ila daga Gaza.

Sai dai Isra’ila da Amurka sun nemi a tsawaita wa’adin zangon farko na yarjejeniyar wanda ya ƙare a watan da ya gabata, ba tare da fayyace yadda za a kawo ƙarshen yaƙin ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Isra ila yarjejeniyar tsagaita tsagaita wutar

এছাড়াও পড়ুন:

HKI Ta Sake Kai Wa Unguwar Dhajiya Dake Beirut Hari

Da safiyar Yau Talata jiragen yakin HKI sun kai hare-hare akan unguwar Dhahiya dake Beirut tare da bayyana cewa ta kai wa wani kusa ne a kungiyar Hizbullah hari.

Harin na yau shi ne irinsa na biyu da HKI ya kai a unguwar Dhahiya tun daga tsagaita wutar yaki a cikin watan Nuwamba na shekarar da ta gabata.

Jiragen yakin na HKI sun yi shawagi a kasa-kasan birnin Beirut kafin aji karar fashewar abubuwa masu karfi.

Kafafen watsa labarai sun ambaci cewa jiragen sun kai harin ne akan wani dogon gini a cikin unguwar.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa ya zuwa yanzu mutane 3 ne su ka yi shahada,yayin da wasu 4 su ka jikkata.

Masu ayyukan ceto sun nufi wurin da aka hai harin, domin daukar wadanda su ka jikkata zuwa abitocin da suke kusa.

Jotunan farko sun nuna yadda gine-ginen da suke yankin su ka illata, biyu daga cikinsu sun rushe baki daya.

Mazauna yankin sun ce, an kai harin ne a lokacin da mutane suke bacci, lamarin da ya haifar da firgici a tsakaninsu.

A ranar Asabar din da ta gabata dai babban magatakardar kungiyar Hizbulllah Sheikh Na’im Kassim ya yi gargadin cewa, Idan HKI ta ci gaba da keta yarjeniyar tsagaita wuta, sannan kuma ba a taka mata birki ba, to suna da zabin abinda za su yi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HKI Ta Sake Kai Wa Unguwar Dhajiya Dake Beirut Hari
  • Gaza : Fiye da mutane 1,000 Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga Maris
  • A Yau Litinin Ce Aka Gudanar Da Sallar Edi Da Bukukuwan Sallah A Nan Iran Da Wasu Kasashen Musulmi
  • Kungiyar RED CROSS Ta Duniya Ta Yi Allawadai Da HKI Saboda Kissan Likitoci 8 A Asbitin Rafah
  • Ƴansanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ɗan Bijilanti A Tawagar Sarki Sunusi II
  • Masar ta miƙa wa Hamas da Isra’ila tayin tsagaita wuta
  • Hamas A Gaza Ta Amince Da Kafa Gwamnatin Hadin Kan Falasdinawa, Amma Makamanta Jan Layi Ne
  • Sin Da Laberiya Sun Kulla Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Ta Fuskar Tattalin Arziki Da Fasaha 
  • Hamas ta yi Tir da kakkausar murya da harin Isra’ila kan masu aikin ceto a Gaza