Gwamnatin Kasar Guinea Ta Yi Wa Musa Dadis Camara Afuwa
Published: 30th, March 2025 GMT
Shugaban gwamnatin soja na kasar Guinea Janar Mamadi Doumbouya ne ya yi wa tsohon shugaban sojan kasar Camara afuwa bayan da aka yanke masa zaman gidan kurkuku bisa laifin kisan kiyashin da ya faru a 2009 a birnin Conakry.
Kafafen watsa labarun kasar ta Guinea ne su ka sanar da afuwar da shugaba Mamadi ya yi wa Camara bisa dalilai na rashin lafiya.
Bugu da kari kakakin fadar shugaban kasa Janar Amara Camara wanda ya yi sanarwar ya ce, an yi hakan ne bisa shawarar da ma’aikatar shari’a ta gabatar.
Camara dai ya mulki kasar ta Guinea ne daga 2008-2009, an kuma yi masa shari’a ne a watan Yuli na 2024, saboda yadda a zamanin mulkin nashi aka yi amfani da karfi wajen murkushe ‘yan hamayya da su ka yi wani taro a cikin filin wasan kwallon kafa.
Fiye da mutane 150 ne dai su ka kwanta dama, kuma jami’an tsaron kasar su ka yi wa mata fiye da 100 fyade.
Shari’ar da aka yi wa Camara wacce ta sami cikakken goyon bayan MDD, ta same shi da lafin gajiyawa wajen hukunta masu laifi.
Matakin na gwamantin yanzu ya biyo bayan shirinta na biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe da kuma yi wa illa.
Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama a kasar suna sa alamun tambaya akan wannan matakin na yi wa adalci Karen tsaye.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Matakin Harajin Kwastam Da Amurka Ta Dauka Babakere Ne
Ya kara da cewa, kowace kasa za ta yi asara idan an gudanar da cinikin duniya bisa ka’idar fin karfi. Sin na fatan kara hadin gwiwa da sauran kasashe don tinkarar kalubale tare da yaki da babakere, ta yadda za su kare muradunsu bisa adalci da daidaito.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp