Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi
Published: 30th, March 2025 GMT
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya musanta cewa akwai tsamin dangantaka tsakaninsa da Gwamnatin Sakkwato.
Ana iya tuna cewa bayan karɓar akalar jagoranci ne Gwamna Ahmed Aliyu ya yi wa Dokar Masarautar Sakkwato gyaran fuska tare da sauke wasu sarakunan gargajiya, lamarin da aka riƙa raɗe-raɗin wani yunƙuri ne tsige shi kansa Sarkin Musulmin.
Sai dai da yake jawabi a saƙonsa na barka da sallah, Sarkin Musulmi ya ce “ba wata rashin jituwa ko faɗa a tsakaninmu.
“Muna aiki tare a koyaushe. Aikinmu mu taimaka wa gwamnatin [Sakkwato] kan shirye-shiryen da ta ɗauko domin ciyar da jama’a gaba.”
Ya yi kira ga al’ummar musulmi da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a domin samun nasara wajen sauke nauyin jama’a da rataya a wuyansu.
Kazalika, Alhaji Sa’ad ya ce karantarwar addini da aka samu a watan Azumi mai albarka abu ne da ya kamata a riƙe a sanya cikin aiki.
“Mu ƙara ɗaure ɗamara kar mu koma gidan jiya wajen aikata saɓon Allah. Mu dage da yin ibada kar a ja baya. Sannan mu riƙa yi wa shugabanni addu’a.
“Ku kuma shugabanni ku ji tsoron Allah cikin jagoranci. Idan za a yi ayyukan jama’a kar a ji tsoron kowa sai Allah,” in ji Sarkin Musulmi.
Sarkin ya yi kira ga jami’an tsaro da su ktara ƙaimi wajen magance matsalar tsaro domin a cewarsa har yanzu akwai sauran aiki a ba iya Jigar Sakkwato kaɗai ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Alhaji Sa ad Abubakar Jihar Sakkwato Sarkin Musulmi Sarkin Musulmi
এছাড়াও পড়ুন:
Marubutan Batsa Ku Ji Tsoron Allah -Emili
To mun san ki a matsayin marubuciyar littafan Hausa. Shin ta ya kika tsinci kanki a duniyar rubutu?
Hukuncin Ubangiji, na yi karance-karance da dama a baya, tun ina karamar secondary na fara rubuta labari a paper a shekarar 2016, idan na rubuta sai na ajiye. Lokacin da muka yi hutu da aka dawo aji na Hudu (a kasar Nijar shekara 4 muke yi a karamar secondary) a karamar secondary a lokacin na fara karantawa kawayena, idan an yi break, to bayan na gama karama secondry na ci gaba da rubutun a paper, a shekara ta 2019 na fara rubutu a yanar gizo har na fara yadawa.
A 2016 mene sunan littafin da kika fara rubutawa?
Gaskiya ba zan iya tunawa ba, don a lokacin ban wani kware a rubutu ba, bayan na gama karanta musu na kan nemi shawararsu a kan yadda labarin zai ci gaba ko abin da ya dace na canza ko sunan da ya dace da labarin.
To wanda kin fara yadawa a yanar gizo cikin shekaran 2019, wanne littafi ne?
Khairat: sunan littafin da na fara fitarwa a 2019 shi ne KHAIRAT. Labarin ya ginu ne don jan kunne ga irin iyayen da suke nacewa sai ‘ƴarsu ta yi karatu kuma a kasashen waje, sai a yi rashin sa’a ita kuwa yarinyar aure take son yi, daga nan rayuwar yaran za ta iya lalacewa, duk da ita Khairat din a nata bangaren ta yi aure ne a boye ba tare da sanin iyayenta ba a kasar da suka aika ta karatu. To bayan Khairat kuma zuwa yanzu na yi wasu littafan guda (14) har da shi ya zama ina da littafai (15) ke nan da na fitar, kuma dukkansu a yanar gizo. Littafan guda Goma Sha Biyar kuwa su ne: Khairat, Nazi’at, Na Yi Asara, Babbar ‘Yar Duniya, Dan Kuka, Mutuwar Aure, Samha, Tura Ta Kai Bango, Gudun Tsira, Dambarwar Aurensu, Dambarwar Abin Dake Raina, Kuskure, Da Wata Kusan, Abin Dake Boye, Kwakwalwar Kifi.
A cikin wadannan littafai guda 15, wanne ne bakandamiyarki?
Labarin ‘Kuskure’ shi ne bakandamiyata. Labari ne da aka gina shi a kan gudun son zuciya, cire kiyayyar wani mutum a rai saboda ba ka san abin da gobe za ta haifar ba. Don gaba da kiyayya ba su da amfani, kuma Manzon Rahama ma ya hane mu a kan zurfafawa a cikin kiyayya.
Kika ce a baya kin yi karance-karancen littafan Hausa. To cikin marubuta na wancan lokacin wace ce gwanarki?
To ai ni har yanzu ban daina karance-karancen Hausa ba. Duk da asalin marubutan sun daina rubutun zube, amma an samu sabbin marubuta. A da gwanata ita ce marubuciya Fauziyya D Sulaiman. A yanzu kuwa zabin tilo a cikin marubuta gare ni zabi ne mai wahala. Sai dai zan iya cewa: a bangaren zamantakewa marubuciya ‘Billyn Abdul’ ce gwanata, idan kuma bangaren horror sai na ce ‘Chamsiya Laouli Rabo’ idan kuma littafin yaki ne to marubuci ‘Mansur Usman Sufi’.
To ko cikin marubuta kina da kawa shakikiyar da kowanne lokaci za a iya samun labarin halin da keki ciki a wajenta?
Kwarai ina da Aunty Fa’iza Abubakar wadda aka fi sani da Maman Afrah.
To ya batun kungiyar marubuta?
Ina cikin kungiyar First Class Writer’s Association wadda tun farkon fara rubutuna antyna Rahama Sabo Usman ita ce ta saka ni a cikinta.
To a matsayinki na tsohuwar makaranciya, ya za ki kimanta marubutan da da kuma na yanzu ta fuskar kwarewa da ilimantarwa?
Babu hadi gaskiya domin kowa akwai matsayinsa, marubutan da sun yi rubutu ne a kan matsalolin da suka shafi al’umma a da, su kuwa marubutan yanzu suna rubutu ne a kan abin da ta shafe mu yanzu, duk da dai yanzu bin ka’idodi da dokokin da adabi ta tanadar ya yi karanci fiye da da can baya saboda yanzu duk wanda ya ga dama zai iya zama marubuci, sai kuma baragurbin marubuta wato marubutan batsa da suka yi yawa a halin yanzu wanda muna tufka su kuwa suna warware wa ne.
To ya batun shiga gasar rubutu?
A duk lokacin da zan ji labarin gasar rubutu bana kasa a guiwa wajen shiga, wasu an yi nasara wasu kuwa ba a yi ba, duk da dai iya shiga gasar ma nasara ce babba. Gasar da na yi nasara kuwa. Akwai gasar da aka shirya a lokacin bikin marubuci Yareema Shaheed gaskiya na manta sunan gidan tb da suka shirya gasar. Sai gasar da kungiyar raya al’adu ta jihar Gombe suka shirya.
Kuma a wanne yanayi ko lokaci kika fi jin dadin yin rubutu?
A duk lokacin da na ci na koshi bana kuma tare da gajiya, sha’awar yin rubutun kan zo mini.
To wadanna nasarori kika cimma a rayuwa ta sanadiyyar rubutu?
Na farko babbar nasara ta ita ce haduwa da mutanen kirki wanda a halin yanzu suke tamkar ‘yan uwana kama daga marubuta har makaranta.
Nasara ta biyu kuma harkar rubutu na saka ni alfahari don a duk inda zan shiga bana jin shakkar kiran kaina da marubuciya. A yanzu kuma bayan fadakarwar da nake yi ina daukar harkar rubutu a matsayin hanyar da zan samu dan na kashewa saboda bunkasar tattalin arzikina.
To wanne kalubale kika fuskanta bayan shigowar ki duniyar rubutu?
Da farko dai kalubalen da na fuskata daga mahaifiyata ne don ina fama da matsalar ciwon ido a lokacin idan na zauna na fara rubutun a waya ko laptop, za ta rika faka a kan ba ki da lafiya amman kullum kina jone da wannan screen ɗin don yin rubuce-rubuce, amman daga baya da rashin lafiyar ya yi sauki sai kawai ta daina mita tana yi min fatan alkairi. Kalubale na gaba kuwa ina son makaranta su rika yi min comment a duk bayan da suka karanta labarina sai dai kuma ba sa yi sai an kai ruwa rana.
Ko wanne kira za ki yi ga ‘yan uwanki marubuta?
Kirana ba zai wuce mu ji tsoron Allah a duk sanda za mu kaura alkalami ba, mu rubuta abin da zai anfane mu ya anfani al’umma, abin da ko da an tambaye ki gobe ba za ki yi da-na-sanin rubuta shi ba, kuma abin da ko ‘ƴarki ko kawarki za ki iya bari ta karanta. Sannan mu rike zumunci da karfafa juna ta hanyar karawa juna sani a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, domin duk inda marubuci yake to fa dan uwanmu ne. Sai kuma marubutan batsa ku ji tsoron Allah.
To wanne sako kike da shi ga masoyanki da suke bibiyar rubuce-rubucenki?
Ina yi wa duk wani masoyina fatan alkairi, da fatan Allah Ya biya masa bukatunsa na alkairi kuma ina mai farin cikin sanar da su zan ci gaba da fadakar da su da kuma nishadantar da su gwargwadon iyawata.
To Hajiya Emilia muna godiya.
Ni ce da godiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp