Shin Mbappe Zai Iya Maye Gurbin Ronaldo A Real Madrid?
Published: 30th, March 2025 GMT
A shekarar 2009 ne Cristiano Ronaldo ya saka hannu akan kwantiragin da ya sa ya zama sabon dan wasan Real Madrid, tun daga wancan lokacin Ronaldo ya jefa kwallaye 311 a wasanni 292 da ya bugawa Madrid, hakazalika ya lashe kofuna 15 a shekaru 9 da ya kwashe a Santiago, to amma yanzu Fionrentina Perez ya dauko wani Bafaranshe daga PSG, wanda yanzu haka ya dauko hanyar doke tarihin Ronaldo a Real Madrid.
Kylian Mbappe ne ya jefa kwallaye 2 a wasan da Real Madrid ta doke Leganes, wanda hakan ya sa ta samu maki daya da abokiyar hamayyarta Barcelona dake saman teburin La Liga, kwallaye biyun da Mbappe ya ci ya sa kwallayen da Mbappe ya ci a kakar wasa ta bana su ka kai 33.
Mbappe Da Bellingham Ba Za Su Buga Wasan Da Real Madrid Za Ta Kara Da Leganes Ba Real Madrid Ta Kwashi Kashinta A Gidan BetisMasu masaukin bakin, wadanda su ka fara wasan ba tare da Vinicius Jr, Rodrygo da Federico Valverde ba sakamakon hutun wasan kasashe da su ka tafi, yanzu sun yi daidai da maki tare da Barcelona wadda ke matsayi na daya da maki 63 a wasanni 29 kafin Barcelona ta buga wasanta na wannan makon tsakaninta da Girona.
Ana hasashen muddin Mbappe ya cigaba da zura kwallaye a ragar abokan karawa, zai iya zarce Ronaldo wajen zura kwallaye duba da cewar har yanzu ba a kammala kakar kwallon kafa ta bana ba, sannan kuma tsohon dan wasan na PSG ya lashe kofunan UEFA Super Cup da kuma FIFA Intercontinental Cup.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
YANZU-YANZU: Gwamnan Edo Ya Kai Ziyarar Jaje Kan Kisan Mafarauta A Uromi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp