Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Legas, Mutane 10 Sun Kamu
Published: 30th, March 2025 GMT
Jihar Lagos ta samu rahoton kamuwar matasa 10 da cutar Mashaƙo tsakanin ranar 1 ga Janairu zuwa 27 ga Maris 2025, yayin da hukumomin lafiya ke ƙara ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar.
Kwamishinan lafiya na Jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana cewa ana iya samun rahoton cutar har sama da 15 a rana. Daga cikin samfurorin da aka yi wa gwaji guda 76 an samu 10 da aka tabbatar da sun kamu, yayin da sauran samfurorin 63 sakamakonsu ya ke lafiya.
Abayomi ya bayyana cewa hukumomin lafiya suna gudanar da aikin tantancewa da bayar da magani cikin gaggawa, Gwamnatin jihar ta ci gaba da samar da tallafi, tare da samar da magani kyauta a asibitoci na gwamnati, inda aka tabbatar da samar da kayan da ake buƙata wajen tattara bayanai da haɗin kai tare da hukumar kiwon lafiya ta ƙasa da ta duniya.
Matakan da aka ɗauka suna tasiri wajen daƙile yaɗuwar ƙwayar cutar a cikin makon nan na baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
NUJ Kebbi Tayi Kiran Ayi Bukukuwan Sallah Lafiya
Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kebbi, NUJ, ta taya gwamnatin jihar da al’ummar musulmin jihar murnar zagayowar ranar Sallah.
Majalisar a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar da Sakatare, Ismail Adebayo, ta yi murna da al’ummar musulmin jihar kan kammala azumin kwanaki 29 na watan Ramadan da kuma bikin Eid-Fitr.
Ta yi kira da a zauna lafiya da juna a tsakanin al’ummar jihar bisa koyarwar addinin Musulunci da manzon Allah mai tsira da amincin Allah tare da la’akari da muhimmancin watan Ramadan da Idi-El-Fitr.
Majalisar ta yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Nasir Idris kan kayayyakin abinci da aka rabawa musulmi a cikin watan azumin Ramadan.
Ta yi kira ga al’ummar jihar da su marawa gwamnati baya a ayyuka daban-daban da ta fara don bunkasa tattalin arzikin jihar da al’ummarta tare da yi musu fatan bukukuwan Sallah lafiya.
PR/Abdullahi Tukur