An Hori Dagatan Kasar Zazzau Su Sa Ido Akan Bakin Fuskokin A Yankunan Su
Published: 30th, March 2025 GMT
Mai martaba Sarkin zazzau,kuma shugaban majalisar sarakunan jihar kaduna, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya bukaci Dagatan da ke masarautar zazzau da su rinka sanya ido sosai akan zirga-zirgar bakin fuskokin da ba su gane ba a cikin su.
Ya yi kiran ne a sakon sa na sallah bayan kammala azumin watan Ramadan a fadar sa dake Zaria.
Ahmed Nuhu Bamalli ya bayyana cewa harkar tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a hakki ne na kowa amma ba gwamnati ita kadai ba,a don haka akwai bukatar ganin an hada karfi da karfe domin samun nasara a game da tsaron.
Mai martaba Sarkin ya kuma bukaci Dagatan da su rinka kai rahoton zuwan duk wani bako ko bakuwa da kuma dalilin zuwan.
Ya ce idan har aka dauki wannan matakin matsalar tsaro za ta ragu sosai,yana mai nuni da cewa sarakunan gargajiya na da muhimman rawar da za su taka game da tsaro.
Haka kuma Sarkin na zazzau ya bukaci iyaye da su rinka sanya ido game da harkokin yau da kullum na ‘ya’yan su.
Haka kuma ya gode wa gwamnan jihar kaduna da shugaban majalisar wakilai,Dr Abbas Tajuddeen, Iyan zazzau saboda irin aiyukan ci gaban da suke samar wa talakawa a zaria da sauran kananan hukumomin jihar kaduna.
A wani labarin kuma,Limamin masallacin juma’a na rukunin kananan gidajen dake kofar Gayan,Zaria, Sheikh Dalhatu Bello Amaru ya yi Allah wadai da kisar Gilla da wasu yan ta’adda suka yi wa wasu mafarauta yan arewa su 11 a Uromi da ke jihar Edo.
Ya yi Allah wadan ne a hudubar sa ta sallar idin karamar sallah da ya gudanar.
Ya ce mutanen Arewa ba su amince da kisar gillar da aka yi wa maharban ba gaira ba dalili.
Sheikh Bello Amaru ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Edo da su tabbatar da ganin an kamo duk mutanen da suka aikata laifin domin suma a kashe su domin ran su bai fi na mafarautar da suka kashe ba tare da wani dalili ba.
Ya yi Bayanin cewa Allah ya bada umurnin cewa duk wanda ya kashe wani shima a kashe shi,amma hakan bai bada damar wani ya dsuki doka a hannun shi ba,hakki ne na hukumomin da abin ya shafa.
Haliru Hamza
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Zargin Takurawa Mataimakin Shugaban Kasa Shettima
Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke nuni da cewa an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, GCON shiga fadar shugaban kasa, inda ta bayyana ikirarin a matsayin shirme, kage da kuma karya gaba daya.
Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa na ofishin mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya sanyawa hannu, ta ce rahoton da wasu shafukan da ba su da tushe suka yada shi, na cikin jerin labaran karya da aka kitsa domin haifar da rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan wani yunkuri ne mai rauni na cin mutuncin mutum da ofishin Mai Girma, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.
Nkwocha ya ce labarin da ake cewa sojoji dauke da makamai sun hana mataimakin shugaban kasa shiga fadar Shugaban kasa wato Villa ba wai kawai an yi ne ba haka kawai, a’a har ma ya nuna rashin fahimtar ayyukan gwamnati.
Sanarwar ta ce, wannan shi ne mafi girman furuci na fatar baka, kuma hakan yana nuni da cewa masu yin wannan tatsuniyoyi sun gaji da zargi da kuma hasashe, in ji sanarwar.
Wannan dai ba shi ne karon farko da fadar shugaban kasar ke yin watsi da irin wadannan rahotannin ba. Kwanaki kadan kafin hakan, ta karyata labaran karya da ke yawo a shafukan yakin neman zabe dauke da hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Fadar shugaban kasar ta yi imanin cewa irin wannan karyar wani yunkuri ne na kawo cikas ga hadin kai da amincin shugabancin kasar.
Mataimakin shugaban kasar ya ci gaba da maida hankali kan ayyukan sa da kuma marawa shugaban kasar baya wajen cimma muradun ‘yan Najeriya. Sanarwar ta kara da cewa, ba shi da wani abin da zai raba hankali.
Nkwocha ya yabawa ‘yan Najeriya da ke ci gaba da nuna goyon bayansu ga gwamnatin Tinubu-Shettima, ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su nemi bayanai daga majiyoyi masu inganci tare da yin taka-tsan-tsan wajen bayar da rahotanni masu ban sha’awa.
Sanarwar ta kara da cewa, “alkwarin da ke tsakanin wannan gwamnati da ‘yan Najeriya ya yiwu ne ta hanyar halaltaccen tsarin mulki.
Bello Wakili