Mutane 9 Sun Mutu Sanadin Haɗarin Mota A Katsina
Published: 30th, March 2025 GMT
A wani hatsarin mota da ya faru a hanyar Malumfashi-Kafur a Jihar Katsina, mutane tara sun rasu yayin da wasu 11 suka jikkata. Hatsarin dai ya shafi wata babbar motar bas da ke ɗauke da fasinjoji 20.
Aliyu Ma’aji, Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Haɗarin ya yi sanadin mutuwar mutane tara da ke cikin wata babbar motar bas mai ɗauke da fasinjoji 20, yayin da aka ceci wasu 11 kuma ana jinyar su a asibiti,” in ji Ma’aji. Ya kuma yi kira ga direbobi su guje wa tuƙin gaggawa, jigilar fasinjoji fiye da kima da kuma rashin kulawa yayin lokutan bukukuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Girgizar Ƙasa: Mutum 1,700 Sun Rasu, 3,400 Sun Jikkata A Myanmar
Hukumomin Myanmar sun buƙaci ƙasashen duniya su hanzarta tura agaji, yayin da jami’an ceto ke ƙoƙarin gano mutanen da suka maƙale a cikin baraguzan gine-gine.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp