Iran: Amurka ta hada kai da Isra’ila wajen kawo cikas ga harkar tsaro a gabas ta tsakiya
Published: 30th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Amurka na da hannu a ayyukan haramtacciyar kasar Isra’ila na yada rashin tsaro da zaman lafiya a yankin.
A wata ganawa da ya yi da Hans Grundberg, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Yemen a birnin Tehran, Araghchi ya yi Allah wadai da ci gaba da hare-haren soji da Amurka ke kaiwa sassa daban-daban na kasar Yeman, wanda ke sanadin mutuwar fararen hula da kuma lalata kayayyakin more rayuwa.
Ya kara da cewa: Hare-haren da sojojin Amurka suke kai wa kasar Yamen, wanda ya zo daidai da irin yadda gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da aiwatar da kisan gilla a zirin Gaza da kuma hare-haren da take kaiwa kasashen Lebanon da Siriya, wata alama ce kawai da ke nuna irin hadin kai da Amurka take yi da Isra’ia wajen rashin bin doka da oda da kuma yadda take da alaka da ayyukan Isra’ila wajen yada rashin tsaro da zaman lafiya a yankin.
Ya bayyana cewa Amurka tana da rashin fahimtar mutanen Yemen, wanda kuma yana da kyau ‘yan siyasar Amurka da su gane cewa ci gaba da mamaye da kisan kiyashi a Falasdinu shine tushen rashin tsaro a yankin.
Dole ‘yan siyasar Amurka su fahimci cewa Amurka ba za su iya da’awar maido da kwanciyar hankali a yankin ba ta hanyar kai hari kan Yemen da kashe mutanen Yemen da ba su ji ba ba su gani ba,” in ji Araghchi.
Ya kara da cewa laifin al’ummar kasar Yaman shi ne hadin kai da goyon bayansu ga al’ummar Palastinu da ake zalunta.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya soki kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kin daukar wani mataki dangane da keta ka’idojin yarjejeniyar MDD da kuma dokokin kasa da kasa da gwamnatocin Amurka da Isra’ila suke yi.
Ya ce ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakai cikin gaggawa don kawo karshen karya doka da rashin mutunta ka’idojin kasa da kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yawan Kayayyakin Da Aka Yi Hada-hadarsu A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Sin A 2024 Ya Ci Gaba Da Kasancewa Na Farko A Duniya
Bayanai da ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta fitar a jiya Asabar sun nuna cewa, a shekara ta 2024, yawan kayayyakin da aka yi hada-hadarsu a tashoshin jiragen ruwa na kasar ya kai tan biliyan 17.6, kuma yawan kwantenan da aka yi hada-hadarsu ya kai miliyan 330, hakan ya sa kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayi na farko ta fannin a duniya.
Har wa yau, daga cikin tashoshin jiragen ruwa 10 da suka fi hada-hadar kayayyaki a duniya, akwai tashoshin jiragen ruwan kasar Sin guda 8, ta fannin hada-hadar kwantenoni kuma, guda 6 na kasar Sin ne. (Mai fassara: Bilkisu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp